IGP Ya Tuna da Iyalan 'Yan Sandan Kano da Suka Rasu a Hatsarin Mota
- IGP Kayode Egbetokun ya ba da diyya ga iyalan ƴan sandan da suka rasu sakamakon hatsarin mota a jihar Kano
- Sufeto Janar na ƴan sandan ya ba da diyyar N10m ga iyalan waɗanda suka rasu tare da N2m ga jani'an da suke jinya a asibiti
- Jami'an ƴan sandan dai sun yi hatsarin ne lokacin da suke kan hanyar dawowa daga zaɓen gwamnan jihar Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - IGP Kayode Egbetokun ya amince da biyan diyyar Naira miliyan 10 ga iyalan jami’an ƴan sanda biyar da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota.
Jami’an sun dawo ne daga zaɓen gwamnan Edo a watan Satumba, lokacin da motarsu ta yi hatsari a garin Karfi da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano.
Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa an sallami takwas daga cikin jami’an 11 da suka samu raunuka a hatsarin, yayin sauran guda uku ke kwance a asibiti.
IGP ya ba da diyyar N10m
Kakakin ya ce Kayode Egbetokun ya kuma amince da biyan N2m ga waɗanda har yanzu ke kwance a asibiti, da kuma N500,000 ga waɗanda aka sallama.
"Sufeto Janar na ƴan sanda ya ɗauki matakin bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa, ta hanyar amincewa da biyan diyyar Naira Miliyan Goma (N10,000,000) ga iyalan waɗanda suka rasu."
"IGP ya kuma amince da biyan N2m ga waɗanda har yanzu suke kwance a asibiti domin samun cikakkiyar kulawa yayin da suke jinya jinya, da kuma N500,000 ga waɗanda aka sallama."
- Olomuyiwa Adejobi
IGP ya janye ƴan sanda a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin janye ƴan sanda daga sakatariyoyin ƙananan hukumomi 23 na jihar Rivers
Umarnin janye ƴan sandan na zuwa ne bayan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng