"Ba Buhari ba ne": An Bayyana Wanda Ya Yi Gaban Kansa Wajen Sauya Fasalin Naira

"Ba Buhari ba ne": An Bayyana Wanda Ya Yi Gaban Kansa Wajen Sauya Fasalin Naira

  • Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Edward Adamu, ya ba da shaida a gaban kotu a shari'ar Godwin Emefiele
  • Edward Adamu ya ce tsohon gwamnan na CBN ya sauya fasalin kuɗin Naira a 2022 ba da amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ba
  • Ya bayyanawa kotun cewa tsohon mai gidansa, Emefiele ya sauya fasalin kuɗin ne ba tare da bin dokoki da ƙa'idojin da aka tanada ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An ci gaba da sauraron shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan sauya fasalin Naira a shekarar 2022.

A yayin shari'ar an gabatar da wani tsohon mataimakin gwamnan CBN, Edward Adamu a matsayin shaida na hudu.

Kara karanta wannan

Buhari ya tura tsofaffin Ministocinsa 10 yin ta'azziya, ya ba iyalan ministarsa shawara

Ana ci gaba da shari'ar Emefiele
An zargi Godwin Emefiele da sauya fasalin Naira Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Edward Adamu ya bayyana a gaban kotun domin ya ba da shaida kan tuhumar da ake yi wa Godwin Emefiele.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na tuhumar Godwin Emefiele

Gwamnatin tarayya na tuhumar Emefiele a gaban kotu kan sauya fasalin Naira da bankin CBN ya yi a ƙarƙashinsa a ƙarshen shekarar 2022.

Tsohon gwamnan na CBN na fuskantar tuhume-tuhume huɗu a gaban mai shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun tarayya da ke Maitama a Abuja.

Da yake bayyana a matsayin shaida na na huɗu a ranar Laraba, Edward Adamu ya shaidawa kotu cewa Emefiele ya saɓa ƙa’idojin da ake da su wajen sauya fasalin Naira a shekarar 2022.

Emefiele ya tsallake Buhari kan fasalin Naira

Edward Adamu ya yi iƙirarin cewa Emefiele ya sauya fasalin kuɗin ne ba tare da amincewar Shugaba Muhammadu Buhari da mahukuntan CBN ba.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya bayyana dalilin barkewar rikici a jihar Rivers

Ana zargin abin da Emefiele ya aikata ya saɓa doka, rahoton Businessday ya tabbatar.

Adamu ya yi zargin cewa Emefiele ya tsallake duk ƙa'idojin da aka tanada kafin a aiwatar da sake fasalin kuɗi.

Ya kuma bayyana cewa takardun kuɗin Naira da ke yawo a yanzu sun bambanta da wanda shugaba Buhari da mahukuntan CBN suka amince da su.

Ya tabbatar da cewa Emefiele ne ya yi waɗannan sauye-sauyen da kansa kurum.

Gwamnan CBN ya magantu kan matatar Dangote

A wani labarin kuma, kun ji babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ƴan Najeriya za su samu sauƙin tsadar sufuri da hauhawar farashin abinci sakamakon fara aikin matatar Ɗangote.

Gwamnan babban banki watau CBN, Olayemi Cardoso ya ce man feturin Ɗangote zai taka rawa wajen rage tsadar sufuri da kayan abinci wanda ake ta kuka da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng