'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane a Hare Haren da Suka Kai Kauyuka Daban Daban
- Ƴan bindiga sun kai hare-hare a ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara da ke jihar Katsina a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- A yayin hare-haren da ƴan bindigan suka kai, sun hallaka aƙalla mutum tara tare da yin garkuwa da wasu mutane masu yawa
- Hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa a ƙauyukan ya sanya manoma kasa samun damar girbe amfanin gonakinsu cikin aminci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane tara tare da raunata wasu da dama a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu mutanen a ƙauyuka daban-daban na ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ce hare-haren sun kawo cikas ga ayyukan noma, lamarin da ya sa mazauna yankin kasa samun damar girbe amfanin gonakinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kai hare-haren
Majiyoyi sun bayyana cewa an kashe mutane huɗu tare da jikkata mutum ɗaya a ƙauyen Ammarawa a wani hari da aka kai da sanyin safiyar ranar Laraba.
A daidai lokacin ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Dan Gani inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu mutum bakwai.
A ƙauyen Tudu, an yi garkuwa da wata mata mai suna Saude da misalin ƙarfe 9:00 na safe.
Tun da farko, a ranar Litinin din da ta gabata, ƴan bindigan sun kashe mutane hudu tare da jikkata wasu a harin da suka kai ƙauyen Kukasheka, da ke karamar hukumar Kankara.
Mazauna yankin sun bayyana rashin jin dadin su, suka koka da yadda ƴan bindiga suka sa ba su iya girbe amfanin gona cikin aminci.
Ƴan sanda za su yi bincike
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, kan lamarin ya yi alkawarin gudanar da bincike kan hare-haren.
Sai dai, ba a a ji daga gare shi ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Lamarin sai addu'a
Idris Hussaini ya shaidawa Legit Hausa cewa ƴan bindiga sun addabi mutanen ƙauyukan Kankara musamman waɗanda suke a Yammaci.
Ya bayyana cewa ƴan bindigan suna kai hare-hare a ƙauyuƙan inda suke takurawa mutane.
"Eh gaskiya ƴan bindiga sun takurawa mutane da hare-hare. Mu kan mu nan yanzu haka amfanin gonar mu mun kasa zuwa mu ciro shi."
- Idris Hussaini
Ƴan bindiga sun farmaki jami'an tsaro
A wani labarin da muka kawo muku a baya, kun ji cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare kan jami'an tsaro a jihar Katsina
Hare-haren da ƴan bindigan suka kai a yammacin ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoban 2024 ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro mutum tara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng