Gwamnan APC Ya Kori Hadiminsa na Musamman, An Gano Dalilin Sallamar
- Mai girma Gwamnan Ondo ya kori ɗaya daga cikin hadimansa kan zargin neman na goro wajen dillalan katako a jihar
- An kori Adebobye Taofiq Ewenla bayan wani faifan sautin muryarsa ya bayyana inda ya nemi a ba shi cin hancin N30m
- Lucky Aiyedatiwa ya kuma umarci a gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa hadimin a kan harkokin gandun daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya kori mataimakinsa na musamman kan harkokin gandun daji (shiryyar sanatan Ondo ta Tsakiya), Adeboye Taofiq Ewenla.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kori Adeboye Taofiq ne bisa zargin neman cin hancin N30m daga wajen masu sayar da katako.
Jaridar Tribune ta ce korar Adeboye Ewenla na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Prince Ebenezer Adeniyan ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar ya ce Gwamna Aiyedatiwa ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa tsohon mataimakin na musamman.
Meyasa gwamnan Ondo ya kori hadiminsa?
The Nation ta ce korar na zuwa ne bayan an fitar da wani faifan sautin muryarsa inda ya buƙaci masu sayar da katako da ke aiki a jihar su ba da N30m.
Ana zargin an ji ya barazanar korar masu katakon daga daji idan har suka kasa biyan kuɗin.
"Gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya kori mataimaki na musamman kan gandun daji (Shiyyar sanatan Ondo ta tsakiya), Mista Adeboye Taofiq Ewenla daga muƙaminsa nan take."
"Hakan ya biyo bayan zargin neman na goro da wasu dillalan katako suka yi wa Mista Adeboye Taofiq Ewenla."
"Gwamna Aiyedatiwa ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike kan ayyukan waɗanda ke da alhakin kula da gandun daji a jihar."
- Prince Ebenezer Adeniyan
Gwamnan Ondo ya naɗa hadimai
A wani labarin da muka kawo muku a baya kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.
Lucky Aiyedatiwa ya amince da naɗa ƙarin hadimai 344 a matsayin mataimaka na musamman da kuma manyan mataimaka na musamman.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng