An Rasa Rai bayan Tashin Wani Abin Fashewa a Jihar Delta
- An samu asarar rai a jihar Delta bayan wani abin fashewa da ba san ko menene ba ya tashi a wurin ƴan bola-bola
- Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu suka samu raunuka, aka garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawa
- Ana tunanin abin fashewar bai wuce tulun iskar gas ko na kashe gobara wanda aka kai wajen ƴan bola-bolan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Wani abin fashewa ya yi sanadiyyar kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu da ba a tantance adadinsu ba a jihar Delta.
Lamarin tashin abin fashewar ya auku ne yammacin ranar Talata, 8 ga watan Oktoban 2024 a garin Sapele na jihar Delta.
Abin fashewa ya tashi a Delta
Jaridar Leadership ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma a wani wurin da ƴan bola-bola ke ajiye kayayyakinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, mai yiwuwa fashewar ta samo asali ne daga fashewar wani tulun iskar gas da ɗaya daga cikin ƴan bola-bolan ya kawo bisa kuskure.
A cewar majiyoyin da ke kusa da wurin, mutumin da ya rasu yana ɗaya daga cikin ƴan bola-bolan da ke wajen bayan ya samu munanan raunuka a jikinsa.
"Aƙalla wasu mutum biyu sun samu munanan raunuka, ciki har da mutanen da ke zaune kusa da wurin. Yanzu haka suna karɓar magani a wani asibiti."
- Wata majiya
Ƴan sanda sun ce wani abu kan lamarin
Wani babban jami’in ƴan sanda, da ya nemi a sakaya sunansa, ya nuna cewa mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin ƴan bola-bolan ya yi amfani da tulun ne cikin rashin sani.
"Mai yiwuwa sun ɗauka cewa wani tsohon ƙarfe ne. Abin da muke tunani shi ne yana iya kasancewa tulun iskar gas ko na kashe gobara."
- Wani jami'in ɗan sanda
Gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a babbar kasuwar Kantin Kwari da ke cikin ƙaramar hukumar Kano Municipal a jihar Kano.
Gobarar wacce ta tashi a daren ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024 ta ƙone shaguna da dama tare da.jawo asara a babbar kasuwar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng