Sojoji Sun Yi Artabu da 'Yan Bindiga, An Samu Asarar Rayuka Masu Yawa

Sojoji Sun Yi Artabu da 'Yan Bindiga, An Samu Asarar Rayuka Masu Yawa

  • Dakarun sojojin sun yi artabu da ƴan bindiga waɗanda suka kai hari a ƙaramar hukumar Ehime Mbano ta jihar Imo
  • Fafatawar da aka yi tsakanin sojojin da ƴan bindigan ta jawo asarar rayuka yayin da wasu kuma suka samu raunuka
  • Lamarin ya jawo mutanen yankin a jihar Imo sun shiga cikin firgici inda suka tsere domin su samu tsira da rayukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Wani ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakanin sojoji da ƴan bindiga a karamar hukumar Ehime Mbano ta jihar Imo.

Artabun ya jawo asarar rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu masu yawa.

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Imo
Sojoji sun yi arangama da 'yan bindiga a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Majiyoyi sun shaidawa jaridar The Nation cewa an kai harin ne a yankin Aba da ke ƙaramar hukumar Ehime Mbano a daren jiya.

Kara karanta wannan

Bayan Sarkin Gobir, wani Basarake ya sake rasuwa a hannun 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun fafata da sojoji

Wata majiya ta bayyana cewa an kashe jami'an tsaro na sojoji a yayin harin da ƴan bindigan suka kai a yankin.

“Wasu ƴan bindiga sun kai hari tare da kashe sojoji da ke yankin a jiya. Duk wurin ya kama da wuta, kuma sojoji sun mamaye ƙauyukan da ke kusa."

- Wata majiya

Dakarujn Sojoji sun firgita mutanen gari

Mazauna garin sun tsere cikin firgici yayin da aka ci gaba da harbe-harbe tsakanin sojojin da ƴan bindigan, lamarin da ya haifar da yanayi na tsoro da rashin tabbas.

"Mun firgita, ƙarar harbe-harbe na ci gaba da amsa kuwwa a kunnuwanmu. Ba mu san abin da zai biyo baya ba. Muna cikin damuwa, Ehime ta kasance wuri mai natsuwa, ba mu san abin da ke faruwa ba yanzu."

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun kai wani harin ta'addanci

- Wani mazaunin garin

Har ya zuwa yanzu dai hukumomin ƴan sanda da na sojoji ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Ƴan sanda sun samu nasara kan ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji rundunar yan sandan Katsina ta samu nasara kan ƴan bindiga masu garkuwa da mutane a ƙananan hukumomi biyu.

Jami'an ƴan sandan sun yi nasarar ceto mutanen da ƴan bindigan suka yi yunƙurin sacewa a kananan hukumomin na Faskari da Dan Musa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng