Zargin Batanci: Daga Bidiyo, Yaron Gwamna Zai Maka Dan Bello gaban Kotu
- Yaron gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala ya yi takaicin yadda Dan Bello ke yada labarin cewa an kama shi a Turai
- A bidiyon da ya saki kan gwamnatin Bauchi da dan gwamnan, Dan Bello ya ce mahukunta a Turai sun damke Shamsuddeen
- Da ya ke musanta cewa an kama shi, Shamsuddeen Bala ya nemi Dan Bello ya bayar da shaida kan labarin da ya ke yadawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Dan gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala ya yi barazana ga fitaccen mai fadakarwa a cikin barkwanci a shafukan sada zumunta, Dr. Bello Galadanci.
Dakta Bello Galadanci da aka fi sani da Dan Bello ya matsa wajen wallafa bidiyo kan rashin kyawun ilimi da lalacewar da harkar lafiya ta yi a jihar Bauchi.
A sakon da dan gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yi mamakin yadda Dan Bello ya bayyana cewa an cafke shi a Turai kan zargin halasta kudin haram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan gwamnan Bauchi ya nemi hujjar almundahana
Jaridar Leadership ta tattaro cewa dan gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala ya nemi tsohon dan jarida, Dan Bello ya fito da shaida kan zargin an cafke shi a Turai.
Ya bayyana cewa a matsayinsa na dan gwamna, idan har mahukunta sun kama shi a kasar waje bisa zargin halasta kudin haram, labari zai karade ko ina.
Dan Bello: Gwamnan Bauchi zai tafi kotu
Shamsuddeen Bala Mohammed ya bayyana cewa zai kai Dan Bello a gaban kotu bisa zargin bata masa suna da yada labaran karya kan shi da mahaifinsa.
Dan Gwamnan ya ce matukar Dan Bello ya gaza kawo cikakkiyar shaida na cewa an kama shi a kasar waje, zai maka shi a gaban kotu domin a bi masa hakkinsa.
An gargadi Dan Bello kan bidiyonsa
A baya mun ruwaito cewa yaron tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir El Rufa'i ya gargadi mai fadakarwa a cikin barkwanci a shafukan sada zumunta, Dan Bello ya bi a hankali.
Bashir El Rufa'i wanda ya bayyana kansa da daya daga cikin masoya Dan Bello, ya na ganin akwai bukatar tsohon dan jaridan ya bi a hankali wajen fadakarwar da ya ke yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng