Gwamna Ya Fadi Illar Gobarar Kantin Kwari ga Kano, Abba Ya Yi wa 'Yan Kasuwa Alkawari
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana alhini kan iftila'in gobarar da ta tashi a Kantin Kwari a karshen makon jiya
- Gobarar ta tashi a gidan Inuwa Me Mai da ke layin Bayajidda a fitacciyar kasuwar kayan da ke jihar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya yan kasuwar alhini, sannan ya bayyana abin da gwamnatinsa za ta yi masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta mika sakon jaje ga yan kasuwar Kantin Kwari da wuta ta konawa kayan da ake zaton sun kai na biliyoyin Naira.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana rashin jin dadin halin da yan kasuwar su ka shiga bayan da gobara ta tashi a ranar Asabar.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya kadu da samun labarin gobarar Kantin Kwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kano ya yi takaicin gobarar K/Kwari
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gobarar wani sashe a Kantin Kwari zai yi illa ga tattalin arziki, kamar yadda daraktan yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafin Facebook.
Ya yi alkawarin taimakon gwamnatin Kano ga yan kasuwar da iftila'in ya shafa, tare da jaddada cewa gwamnati na tare da su a cikin alhinin wannan lamari.
"Masu kashe gobara sun kokarta:" Gwamnan Kano
Gwamnatin jihar Kano ta yaba da yadda masu aikin kashe gobara su ka yi namijin kokari wajen dakile yaduwar gobara da ta tashi a Kantin Kwari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma shawarci yan kasuwa su kara sa ido wajen kaucewa duk abin da zai iya jawo gobara a nan gaba.
Gobara a Kano: Aminu Ado Bayero ya jajanta
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ziyarci kasuwar Kantin Kwari domin jajantawa yan kasuwa bisa iftila'in gobara.
Gobarar da ta tashi a gidan Inuwa Me Mai layin Bayajidda ta lakume dukiyoyi, amma jami'an kashe gobara na jiha da tarayya sun kai dauki a kan lokaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng