IGP Ya Dauki Mataki bayan Gwamna Fubara Ya Rantsar da Ciyamomi a Rivers

IGP Ya Dauki Mataki bayan Gwamna Fubara Ya Rantsar da Ciyamomi a Rivers

  • Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya, ya umarci janye jami'an hukumar daga sakatariyoyin ƙananan hukumomin jihar Rivers
  • Kayode Egbetokun ya jibge jami'an ƴan sandan ne bayan rigimar shugabanci ta ɓarke a ƙananan hukumomin a cikin watan Yuni
  • Umarnin buɗe sakatariyoyin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da sababbin ciyamomi 23 a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin janye ƴan sanda daga sakatariyoyin ƙananan hukumomi 23 na jihar Rivers.

A watan Yuni ne dai aka rufe sakatariyoyin sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar da waɗanda Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa a matsayin na riƙo.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane 7 da suka sace

IGP ya janye 'yan sanda a Rivers
IGP ya janye 'yan sanda daga sakatariyoyin kananan hukumomin Rivers Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Litinin, jami'ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan jihar Rivers, SP Grace Iringe-Koko, ta ce sabon kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Bala Mustapha, ya umarci a janye ƴan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa IGP ya umarci a janye ƴan sandan?

Kakakin ƴan sandan ta ce umarnin janye ƴan sandan ya fito ne daga wajen Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Grace Iringe-Koko ta ce matakin ya yi daidai da ƙudirin rundunar ƴan sandan Najeriya na zama ƴan ba ruwanmu da tabbatar da gudanar da ayyukan dimokuraɗiyya ba tare da wata tangarɗa ba.

"Sufeto Janar na ƴan sanda ya bayar da umarnin a buɗe sakatariyoyin ƙananan hukumomin waɗanda ƴan sanda suka tsare a baya."
"Za a sake tura ƴan sanda ne kawai zuwa waɗannan wuraren idan aka samu wata matsala ko rashin bin doka da oda, inda za a gaggauta ɗaukar matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban basarake da wasu mutane a Kebbi

- Grace Iringe-Koko

Umarnin janye ƴan sandan na zuwa ne bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da sababbin shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Gwamna Fubara ya lallasa Wike a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya dawo da ikon mulkin ƙananan hukumomi a hannunsa daga magabacinsa, Nyesom Wike.

Masu biyayya ga Fubara da suka fafata zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar Action Peoples Party (APP) sun samu nasarar lashe kujerun ƙananan hukumomi 22 cikin 23.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng