Wasu Miyagu Sun Buɗe Wuta a Kusa da Gidan Ministan Tinubu, Sahihan Bayanai Sun Fito

Wasu Miyagu Sun Buɗe Wuta a Kusa da Gidan Ministan Tinubu, Sahihan Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun nuna cewa an yi harbe-harbe a gundumar Rumuepirikom, kusa da gidan ministan Abuja, Nyesom Wike a jihar Ribas
  • Wata majiya daga yankin ta ce tun da sassafe wasu mutnae suka yi wa mazauna yankin gargaɗin kar su fito zaben kananan hukumomin yau Asabar
  • Mutum ɗaya ya samu rauni sakamakon harbe-harben da aka yi wanda tuni aka kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Mutane sun shiga tashin hankali yayin da aka fara harbe-harbe ba kakkautawa a gundumar Rumuepirikom, mahaifar ministan Abuja, Nyesom Wike.

Wata majiya daga yankin ta ce tun safe wasu mutane suka zo yankin suka sanar da cewa kada wanda ya kuskura ya fito kaɗa kuri'a a zaɓen da ake yi yau Asabar.

Kara karanta wannan

AKISIEC: Yan daba sun tafka ta'asa, sun bankawa ofishin hukumar zaɓe wuta

Nyesom Wike.
An fara harbe-harbe a gundumar Wike ranar zaɓen ƙananan hukumomi a Ribas Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Twitter

A rahoton da Vangaurd ta tattaro, lokacin da malaman zaɓe suka kama hanyar zuwa anguwar da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor, an ga ƴan bindiga sun isa yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu tsageru sun yi harbe-harbe a Fatakwal

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigar da ba a san ko su waye ba, sun buɗe wuta tare da tsorata mazauna yankin, inda suka gargarɗe kar su fito yin zaɓe.

Channels tv ta ce an ga wasu mutane a cikin wata bakar motar Toyota Corolla ɗauke da bindigu suna harbe-haɗbe a yankin Wimpy, kusa da gidan Wike.

Wike: Mutum 1 ya samu rauni

Rahotanni sun nuna cewa mutum ɗaya ya samu rauni sakamakon harbe-harben kuma tuni aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.

Wannan lamari na tashin hankali na zuwa ne yayin da zaɓen ciyamomi da kansiloli ya kankama a faɗin jihar Ribas duk da hukuncin kotu na dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gama tsara sunayen ministocin da zai kora daga aiki, bayanai sun fito

Bam ya tashi a sakatariyar APC

A ɗazu kun ji cewa wasu da ake zargin ƴan daba ne sun tayar da ababen fashewa a sakatariyar jam'iyyar APC da ke birnin Port-Harcourt na jihar Rivers.

Lamarin ya auku ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024 yayin da ake shirin zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262