Gwamnatin Uba Sani Ta Ciyo Bashin N36bn a Kaduna? An Gano Gaskiya

Gwamnatin Uba Sani Ta Ciyo Bashin N36bn a Kaduna? An Gano Gaskiya

  • Gwamnatin jihar Kaɗuna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta ciyo bashin N36bn
  • Gwamnatin ta bayyana cewa tun bayan zuwanta kan karagar mulki, yanzu ba ta ciyo bashin ko sisin kwabo ba
  • Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi na jihar, Mukhtar Ahmed ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tun kafuwar gwamnati mai ci a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani ba ta karɓo wani sabon bashi ba.

Gwamnatin ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta ciyo bashin Naira biliyan 36 a cikin watanni shida da suka gabata, inda ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin 'yan bindiga: Sanata ya yiwa Gwamnan PDP martani mai zafi

Gwamna Uba Sani ya musanta ciyo bashi
Gwamnatin Kaduna ta musanta ciyo bashin N36bn Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi na jihar, Muktar Ahmed ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnati ta ce kan ciyo bashin?

Kwamishinan ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta yi karin haske kan basussukan da ake bin jihar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Gwamnatin ta bayyana cewa a zahiri tana biyan adadi kusan sau uku na bashin da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo saboda faɗuwar darajar Naira.

Kwamishinan ya bayyana cewa ko shakka babu faɗuwar darajar Naira za ta ci gaba da shafar biyan bashin da aka gada a wajen gwamnatin da ta gabata.

Gwamnatin ta bayyana cewa basussukan da aka gada daga gwamnatin da ta gabata suna da dogon lokaci.

"Waɗannan basussukan da suka haɗa da shirye-shiryen bankin duniya kamar su AGILE, SURWASH, da ACRESAL, duk an amince da su a zamanin gwamnatin da ta gabata."

Kara karanta wannan

Gwamna ya roƙi Tinubu ya kawo masa agaji, ambaliya ta ci garuruwan Arewa 70

- Mukhted Ahmed

Uba Sani ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan matsalolin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar nan.

Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnati tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da ke addabar ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng