Daukar Nauyin 'Yan Bindiga: Sanata Ya Yiwa Gwamnan PDP Martani Mai Zafi
- Sanata Shehu Umar Buba ya yi martani kan zargin da gwamnan Bauchi ya yi masa na ɗaukar nauyin ƴan bindiga
- Sanatan ya bayyana cewa zargin na Gwamna Bala Mohammed ba komai ba ne face tsantsagwaron ƙarya mai cike da ƙage
- Ya caccaki Gwamna Bala kan yadda yake ci gaba da fitowa yana cin mutuncin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Shehu Umar Buba, ya yiwa gwamnan Bauchi martani kan zargin ɗaukar nauyin ƴan bindiga.
Sanatan ya bayyana zargin na Gwamna Bala Mohammed a matsayin mara tushe kuma ƙage ne tsantsagwaronsa.
Sanatan, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro da leƙen asiri na majalisar dattawa, ya tabbatar da cewa ba zai ji tsoron irin waɗannan ƙarairayin ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane martani sanatan ya yi?
A wata sanarwa da hadiminsa, Hassan Gajin Duguri ya fitar, Sanata Shehu Umar Buba ya bayyana ƙararsa da gwamnan ya kai ga shugaban ƙasa Bola Tinubu a matsayin abin dariya da nadama, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Sanatan ya ce da bai yi niyyar mayar da martani ga wannan zargi maras tushe ba amma ya ga ya zama dole ya fito ya bambance tsakanin ƙarya da gaskiya.
Ya caccaki Gwamna Bala Mohammed kan yadda yake ci gaba da zagi da cin mutuncin Shugaba Tinubu yayin da yake tunzura ƴan Najeriya kan gwamnatin tarayya.
"Gwamna Bala Mohammed ya ƙaddamar da yaƙin siyasa da Sanata Buba da sauran waɗanda suka ƙalubalanci salon shugabancinsa da girman kansa."
"Sanata Buba ya jajirce wajen ƙaryata waɗannan zarge-zarge marasa tushe tare da jaddada aniyarsa na yiwa al’ummar mazaɓarsa hidima da tabbatar da tsaron ƙasa."
- Hassan Gajin Duguri
Gwamna Bala zai yi gyara a fada
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da gyara tare da inganta fadojojin sarakunan gundumomi 11 na karamar hukumar Dass da ke a jihar.
Gwamnan ya kuma amince da sake gyara fadar mai martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Othman, a ci gaba da sauye-sauyen da ake samu a masarautun gargajiya a jihar.
Asali: Legit.ng