Lantarki Ta Babbaka Ɓarawo da Aka Dawo da Wuta Yana Satar Waya

Lantarki Ta Babbaka Ɓarawo da Aka Dawo da Wuta Yana Satar Waya

  • Wani matashi dan shekaru 34 ya hadu da mugun tsautsayi yayin da aka dawo da wuta yana kokarin satar wayar lantarki
  • An ruwaito cewa matashin mai suna John Pere ya shahara da satar wayar wutar a wurare da dama kafin dubunsa ta cika
  • 'Yan Sandan jihar Delta za su gudanar da bincike kan lamarin domin gano ko akwai wadanda suke hada kai wajen satar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Wutar lantarki ta babbaka wani matashi da ake zargin yaje satar waya kuma ya yi rashin sa'a aka dawo da wuta.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis da sassafe a wani waje kusa da matatar man Najeriya da ke Warri.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Delta
Wuta ta kona barawon wayar lantarki a Delta. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa wayar da aka zargi matashin da sacewa mallakar kamfanin rarraba wuta ne na BEDC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wutar lantarki ta babbaka ɓarawo a Benin

Wani matashin mai suna John Pere ya samu mummunan kuna yayin da wuta ta dawo yana ƙoƙarin satar wayar lantarki.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa John Pere ya fado daga sama yana karkarwa a kasa jikinsa duk ya babbake.

John Pere ya saba satar wayar lantarki

An ruwaito cewa matashin ne ya fitini yankin Obodo na jihar Delta da satar wayar wuta a kwanakin baya.

Wata majiya ta tabbatar da cewa a baya John Pere ya kasance yana satar danyen mai amma daga baya ya dawo satar wayar wutar lantarki.

Kamfanin BEDC ya yi karin haske

Kakakin kamfanin raba wutar lantarki na BEDC, Esther Okolie ta ce da barawon ya yi nasarar yanke wayar da ya jefa al'umma cikin duhu a yankin.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu bayan sace jariri dan kwanaki 7 a gidan suna

Rundunar yan sanda a jihar ta ce za ta yi bincike domin tabbatar da ko akwai wadanda ɓarawon yake sata tare da su.

Yan ta'adda sun sake lalata layin wuta

A wani rahoton, kun ji cewa yan ta'adda sun sake kai farmaki kan layin samar da wutar lantarki da ya taso daga Gombe-Maiduguri-Damaturu.

An ruwaito cewa wannan ne karo da uku da yan ta'adda ke lalata hanyar samar da wuta a yankin a cikin yan watannin nan babu kakkautawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng