Tsohon Gwamna Ya Caccaki Tinubu kan Tafiya Hutu Kasar Waje

Tsohon Gwamna Ya Caccaki Tinubu kan Tafiya Hutu Kasar Waje

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya yiwa shugaban ƙasa Bola Tinubu wankin babban bargo bayan ya shilla zuwa ƙasar Burtaniya
  • Sule Lamido ya caccaki matakin da Tinubu ya ɗauka na tafiya hutun kwanaki 14 yayin da ake ci gaba da fama da matsin rayuwa ƙasar nan
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa da gangan Shugaba Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin halin ƙunci da wahalar da suke fama da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi martani kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na tafiya hutu a ƙasar waje.

Sule Lamido ya caccaki shugaban ƙasan kan tafiya hutun sati biyu da ya yi a birnin Landan da ke ƙasar Burtaniya.

Kara karanta wannan

Maulidi: Gwamnan Neja ya nuna takaici bayan jirgi ya kife da mutane sama da 300

Sule Lamido ya caccaki Tinubu
Sule Lamido ya caccaki Shugaba Tinubu Hoto: Sule Lamido, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook bayan an sanar da cewa Tinubu ya shilla zuwa birnin Landan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido ya caccaki Tinubu

Jigon na jam'iyyar PDP ya yi zargin cewa da gangan Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin halin ƙunci da tsadar rayuwa.

"Shugaba Bola Tinubu ya tafi ƙasar waje domin yin tunani a kan manufofin sauya tattali arziƙi na gwamnatinsa."
"Yana sane da gangan ya ƙaƙabawa ƴan Najeriya wahala, raɗaɗi da baƙin ciki."
"Shin yana da tausayi, ƙauna, kulawa, da damuwa domin yin tunani game da mummunan halin da ƴan Najeriya ke ciki yayin da yake cikin jin daɗi a Turai?"
"A can baya an taɓa yin Fir’auna, kuma an taɓa yin Musa."

- Sule Lamido

A ranar Laraba ne dai fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Tinubu zai je hutun sati biyu a birnin Landan na ƙasar Burtaniya.

Kara karanta wannan

Murnar 'yancin kai: Muhimman abubuwan da za a tuna da su daga jawabin Tinubu

Sule Lamido ya soki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jami'yyar adawa ta PDP, Sule Lamido ya caccaki salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sule Lamido ya ce lallai akwai kura-kurai a tsarin jam'iyyar APC wanda hakan ne ya kai Najeriya halin da take ciki na matsin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng