Maulidi: Gwamnan Neja Ya Nuna Takaici bayan Jirgi Ya Kife da Mutane Sama da 300

Maulidi: Gwamnan Neja Ya Nuna Takaici bayan Jirgi Ya Kife da Mutane Sama da 300

  • Gwamnan Neja ya nuna kaɗuwarsa kan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a jihar wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane
  • Mai girma Umaru Bago ya bayyana hatsarin a matsayin babban abin takaici wanda ke cike da baƙin cikin rasa rayuka
  • Ya kuma jajantawa mutanen ƙaramar hukumar Mokwa tare da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnan Neja, Umaru Bago ya nuna baƙin cikinsa kan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar.

Gwamna Bago ya bayyana hatsarin jirgin ruwan a matsayin abin takaici mai cike da baƙin ciki.

Gwamna Bago ya yi ta'aziyya a Neja
Gwamna Bago ya kadu kan hatsarin jirgin ruwa a Neja Hoto: Hon. Umaru Mohammed Bago
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Gwamna Bago ya bayyana hakan ne cikin saƙon ta’aziyyar da ya yi wanda babban sakataren yada labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar.

Kara karanta wannan

Faɗa ya kaure, manyan ƴan bindigan Arewa da yaransu akalla 20 sun baƙunci lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago ya yi ta'aziyyar hatsari

Gwamna Bago ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake samun yawaitar haɗuran jirgin ruwa a cikin ƴan shekarun nan a jihar.

Ya bayyana yawaitar haɗuran da ake samu a matsayin abin damuwa, inda ya ƙara da cewa gwamnati za ta ruɓanya ƙoƙarin da take yi na tabbatar da ana bin ƙa’idojin matakan kariya domin daƙile aukuwar hakan a gaba.

Gwamnan wanda ya jajantawa shugabanni da al’ummar ƙaramar hukumar Mokwa bisa aukuwar lamarin, ya kuma jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, rahoton da tashar AIT ya tabbatar.

Gwamna Bago ya yi addu’ar Allah ji kan waɗanda suka rasu, ya ba iyalansu haƙuri da juriya sannan ya ba waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.

An gano gawarwarkin hatsarin Neja

A wani labarin kuma, kun ji masu ninkaya a Neja sun gano karin mutane takwas daga cikin masu zuwa maulidi da kwalekwalensu ya kife a makon nan.

Kara karanta wannan

NSEMA: An bayyana halin da ake ciki bayan jirgin ƴan Maulidi ya yi hatsari

Mutane akalla 300 ne su ka hau wani jirgin ruwa daga yankin Mundi, inda jirgin ya kife a Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.

An samu nasarar zaƙulo wasu daga cikin gawarwakin mutane sama da 150 da suka rasu bayan jirgin ya kife.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng