Gwamnan APC Ya Ba da Hutu a Ranar Juma'a a Jiharsa, Ya Fadi Dalili

Gwamnan APC Ya Ba da Hutu a Ranar Juma'a a Jiharsa, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnatin jihar Benue ta ba da hutu domin zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar a ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024
  • Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Hyacinth Alia ta ayyana ranar Juma'a, 4 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar hutu
  • A wata sanarwa da aka fitar, Alia ya bayyana cewa ya ba da hutun domin ba masu kaɗa ƙuri'a damar zuwa ƙananan hukumominsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ƙarƙashin jagorancin Hyacinth Alia ta ayyana ranar Juma'a, 4 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu.

Gwamnatin ta ba da hutun ne gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar, Asabar 5 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da hutu a ranakun Alhamis da Juma'a a jiharsa, bayanai sun fito

Gwamnan Benue ya ba da hutu
Gwamna Alia ya ba da hutu a Benue Hoto: Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Gwamna Alia ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Tersoo Kula, ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Alia ya ba da hutu?

Gwamnan ya ce an ba da hutun ne domin ba da dama ga masu kaɗa ƙuri'a su je ƙananan hukumominsu domin gudanar da zaɓen, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ya jaddada muhimmancin shiga zaɓen sannan ya kuma ƙarfafa gwiwa ga dukkanin mutanen jihar da su yi amfani da wannan ranar da ba a aiki wajen sauke nauyin da ke wuyansu na zaɓar shugabanni.

Gwamna Alia ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa tare da jajircewa za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da adalci

Alia ya kuma buƙaci mutanen jihar da su ba da fifiko kan zaman lafiya da haɗin kai a lokacin zaɓen.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram

Ɗan majalisa zai maka gwamna kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa honorabul Terseer Ugbor mai wakiltar mazaɓar Kwande/Ushongo a majalisar wakilai ta ƙasa ya ɗauki zafi kan laƙaba masa zargin karkatar da kayan tallafi.

Ɗan majalisar wanda ya fito daga jihar Benue a Arewa ta Tsakiya ya buƙaci lauyoyinsa su shirya maka Gwamna Hyacinth Alia da gwamnatinsa a kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng