Matawalle vs Dauda: An Bayyana Kuskuren da Gwamnan Zamfara Ke Yi Kan Rashin Tsaro

Matawalle vs Dauda: An Bayyana Kuskuren da Gwamnan Zamfara Ke Yi Kan Rashin Tsaro

  • Deyemi Saka ya nuna kuskuren da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal yake yi kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar
  • Mai sharhi kan al'amuran na jama'a ya bayyana cewa gwamnan yana sanya siyasa a cikin matsalar rashin tsaron
  • Ya bayyana cewa bai dace ba Gwamna Dauda ya riƙa zargin magabacinsa, Bello Matawalle da hannu a matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Deyemi Saka, ya yi magana kan taƙaddamar da ake yi tsakanin Gwamna Dauda Lawal da Bello Matawalle kan rashin tsaro a Zamfara.

Deyemi Saka ya bayyana zargin da Gwamna Dauda ya yi na cewa Matawalle ne ya haddasa tabarbarewar tsaro a jihar Zamfara a matsayin mara tushe ballantana makama.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

An caccaki Gwamna Dauda Lawal
An caccaki Gwamna Dauda kan sukar Matawalle Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Deyemi Saka ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi kan rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma a wani shirin talabijin da aka yi a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane kuskure Gwamna Dauda yake yi?

Ya bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal yana sanya siyasa a cikin matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar da yake mulki.

Ya ce a maimakon zarge-zarge marasa tushe, ya kamata a yabawa Matawalle bisa yadda ya jagoranci sojoji wajen kashe shugabannin ƴan bindiga 14 cikin 18 da ke ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma cikin ƙanƙanin lokaci.

"Iƙirarin da Dauda Lawal ya yi na ƙoƙarin da yake yi kan yaƙi da rashin tsaro a jihar Zamfara ya samo asali ne daga ƙarya. Bai kamata ya riƙa ƙoƙarin ɓata sunan Matawalle ba."
"Rundunar tsaron jihar da yake cewa ya ƙaddamar, Matawalle ne ya samar da ita a lokacinsa. Ko kuwa yana sake ƙaddamar da rundunar tsaron da dama can akwai ta tun kafin a rantsar da shi?"

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Ana murnar samun ƴanci, gwamna ya ƴanta fursunoni a Najeriya

- Deyemi Saka

Ƙungiya ta goyi bayan Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Arewa Peace Foundation (APF) ta nuna goyon bayanta ga Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara.

Ƙungiyar APF ta buƙaci masu sukar gwamnan da masu ruwa da tsaki su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, su haɗa kai da shi wajen dawo da zaman lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng