Ana Fama da Wahala, Gwamna Ya Rabawa Manyan Sarakunan Arewa 4 Motocin Alfarma
- Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya bai wa sarakuna huɗu masu daraja ta farko manyan motoci
- Da yake miƙa masu mabuɗan motocin, gwamnan ya ce yana sane da rawar da suke takawa wajen samar da tsaro da ci gaba
- Nasir Idris ya ce gwamnatinsa ta ba ƴan majalisa da kwamishinoni motoci, yanzu kuma ta zaɓi sarakuna iyayen ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya bai wa sarakuna huɗu sababbin motoci domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Gwamnan ya ba kowane sarki daga cikin sarakuna guda huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar Kebbi motar Toyota Land Cruiser yau Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2024.
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Gwamna Idris ya miƙawa sarakunan makullan motocin a wani taro da aka shirya a Birnin Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wurin, Ƙauran Gwandu ya ce ya ba su motoci ne domin ƙara gode masu bisa rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Jerin sarakunan da gwamna ya ba motoci
Hukumar dillancin labarai NAN ta ce sarakunan da aka ba motocin su ne sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu-Bashar da sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad-Mera.
Sauran sun haɗa da Sarkin Yauri, Dr Muhammad Zayyanu-Abdullahi; da kuma Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani-Sami, kamar yadda Guardian ta kawo.
Dalilin ba sarakuna motoci a Kebbi
Da yake jawabi, Gwamna Idris ya ce:
"Masu martaba, gwamnatina na sane da gudummuwar da kuke bayarwa, mun ba ƴan majalisar dokoki, kwamishinoni, hukumomin tsaro da shugabannin hukumomin gwamnati motoci.
"Amma kowa ya san matsalolin da iyayen kasa sarakuna ke fuskanta wajen tafiye-tafiye saboda motocinku duk sun tsufa. Motocin da muka baku yanzu irinsu gwamna ke hawa."
"Duk inda kuka je da waɗannan motoci za a riƙa girmama ku a matsayin sarakuna masu daraja daga jihar Kebbi.
Ambaliya ta ci mutane a Kebbi
Kuna da labarin ambaliyar ruwa ta laƙume rayukan mutum 29 tare da lalata dubban gidaje da gonaki a ƙananan hukumomi 16 a Kebbi.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Yakubu Ahmed ya ce ruwan ya rusa gidaje 321,000 da gonakin mutane 858,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng