NSEMA: An Bayyana Halin da Ake Ciki bayan Jirgin Ƴan Maulidi Ya Yi Hatsari
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja ta yi bayanin halin da ake ciki bayan kifewar jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji kusan 300
- Shugaban NSEMA, Abdullahi Baba-Arah ya ce zuwa yanzu an yi nasarar ceto mutum 150 amma bai faɗi waɗanda suka mutu a ciki ba
- Ya ce har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba wanda ya auku a daren ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 za a je wajen taron maulidi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Neja - A ɗazu ne aka samu labarin hatsarin jirgin ruwa a ƙauyen Gabjibo da ke ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Neja.
Rahotanni sun nuna jirgin ruwan ya nutse da ƴan Maulidi kusan mutum 300 kuma ana fargabar akalla 150 daga cikin sun riga mu gidan gaskiya.
Bayan haka ne hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja watau NSEMA ta fitar da bayanan halin da ke ciki a ƙoƙarin ceto mutanen, tashar Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatsarin Neja: An ceto mutum 150
Darakta janar na hukumar NSEMA, Alhaji Abdullahi Baba-Arah ya ce zuwa yanzu an samu nasarar ceto mutum 150 da hatsarin jirgin ya rutsa da su, in ji Vanguard.
Ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon ɗaukin gaggawa da mutanen yankin suka kai, inda waɗanda suka iya ruwa suka fara aikin ceto a kan lokaci.
Ya ce har yanzu ba a gano musabbabin faruwar lamarin ba, yana mai karawa da cewa ana ci gaba da kokarin lalubo sauran mutanen da hatsarin ya rutsa da su a kogin.
"Jirgin ruwan ya dauko fasinjoji kusan 300 galibi mata da kananan yara, kuma sun taso ne daga kauyen Mundi da nufin zuwa taron Maulidi a ƙauyen Gbajibo.
"Hukumar za ta ci gaba da bayar da cikakken bayani kan halin da ake ciki," in ji shugaban NSEMA.
Mutum nawa suka mutu a hatsarin?
A sanarwar da sakataren yada labarai na karamar hukumar Mokwa, Abubakar Dakani ya fitar, jirgin na dauke da fasinjoji sama da 300 a lokacin da ya kife.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar, Abdullahi Muregi ya tabbatar da gano gawarwaki kusan 60, yayin da aka samu wasu 10 da suka tsira.
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Zamfara
A wani rahoton kuma wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu tarin yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane sama da 40 ne suka rasu sakamakon hatsarin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Gummi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng