Tinubu zai Tafi Hutu Kasar Waje, an Bayyana Kwanakin da Zai Yi

Tinubu zai Tafi Hutu Kasar Waje, an Bayyana Kwanakin da Zai Yi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya domin tafiya hutu kasar Birtaniya a yau Laraba, 2 ga watan Oktoba
  • Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar zai tafi hutun ne na tsawon mako biyu bayan hutun da ya saba duk shekara
  • Ana sa ran cewa Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya ne a ranar 16 ga watan Oktoba da zarar ya kammala hutun da ya dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni daga fadar shugaban kasa na nuni da cewa Bola Ahmed Tinubu zai tafi hutu.

Shugaba Bola Tinubu zai tafi hutu ne zuwa birnin London na kasar Birtaniya kuma zai shafe kwanaki 14.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai tafi hutu London. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa shugaban kasar zai dawo Najeriya ne a ranar 16 ga watan Oktoban da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zuwan Tinubu London

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Bola Tinubu zai tafi London ne domin nazari kan tsare tattalin arziki da ya kawo Najeriya.

Tsare tsaren Bola Tinubu sun jawo tsadar rayuwa a Najeriya wanda hakan ya jawo zanga zanga a fadin kasar.

Rahoton Pulse Najeriya ya nuna cewa a yau Laraba ne shugaban kasar zai tashi daga Abuja zuwa birnin London.

Tsare tsaren gwamnatin Tinubu

Tun zuwam Tinubu mulki a 2023 ya fara kawo wasu tsare tsaren tattalin arziki kamar cire tallafin man fetur.

Gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin lantarki tare da karya darajar Naira a cikin tsare tsaren farfado da tattalin arzikin Najeriya.

A yanzu haka dai yan Najeriya sun zuba ido domin ganin abin da shugaban kasar zai ce bayan nazari kan tsare tsarensa.

Kara karanta wannan

'Ba a saurare shi ba,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan jawabin 1 ga watan Oktoba

Yan majalisa sun ja da Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisar wakilai sun nuna kin amincewa da lambar girma ta CFR da Bola Tinubu ya ba shugabansu, Rt. Hon. Abbas Tajudeen.

Yan majalisar sun bayyana cewa ba za su yarda da nuna bambanci tsakanin shugabansu da shugaban majalisar dattawa ba wajen girmamawa.

A ranar Talata ne aka fitar da sanarwa kan lambar girma da shugaban kasa zai ba wasu manyan mutane ciki har da mai girma Abbas Tajudeen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng