Bayan Shekaru 2 da Daina Aiki, 'Dan Asalin Kano Ya Tuko Jirgin Emirates zuwa Najeriya
- Kamfanin jirgin sama na kasar UAE, Emirates ya dawo da jigilar fasinjojin zuwa Najeriya bayan shekaru biyu
- Emirates ya dakatar da jigila a kasar nan tun a shekarar 2022 bayan samun wani sabani da gwamnatin tarayya
- A makon nan wani dan asalin jihar Kano, Kyaftin Mohammed Madugu ne ya tuko jirgin farko na kamfanin wajen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - A ranar Talata ne dan asalin jihar Kano, Kyaftin Mohammed Madugu ya tuko jirgin Emirates na farko zuwa Najeriya a cikin shekaru biyu.
Jirgin Emirates ya yi jigilar karshe tsakanin Legas zuwa Abuja a ranar 30 Satumba, 2022 bayan an samu sabani da kasar nan kan wasu kudi da ya ke bin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jirgin na hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ya dauki matakin saboda rashin mayar masa da kudin da su ka kai $80m.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Emirates: Sabani tsakanin UAE da Najeriya
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta hana bayar da biza ga yan kasar nan saboda sabanin da ke aka samu.
Rashin kyawun alakar ya sa jirgin kasar nan na Air Peace da sauran jirage sun daina jigilar fasinjoji daga kasar nan zuwa hadaddiyar daular Larabawar.
An sasanta sabanin Najeriya da UAE
Rahotanni sun tabbatar da yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci neman sasanci da UAE na a dawo da jigilar jirgin.
Bayan gwamnatin tarayya ta biya kudin jiragen saman kasashen ketare na $900m, an gudanar da taruka da jirgin Emirates da UAE kan dawo da alakar da ke tsakaninsu.
Najeriya: Jirgin Emirates ya dakatar da jigila
A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin Emirates, ya dakatar da jigilar fasinjojin Najeriya bayan hana ba 'yan kasar izinin shiga UAE.
Kamfanin jirgin saman Emirates ya koka kan kudin da ya ki bin Najeriya na miliyoyin daloli da ba'a biya ta ba wanda yawansu ya kai akalla $80m.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng