Muhimman Abubuwan Tunawa 3 da Suka Faru a Ranar da Najeriya Ta Samu Ƴanci Kai

Muhimman Abubuwan Tunawa 3 da Suka Faru a Ranar da Najeriya Ta Samu Ƴanci Kai

A ranar 1 ga watan Oktoba na kowace shekara, giwar Afirka kuma kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, Najeriya, ke murnar ranar samun ƴancin kai.

Ƙasar mai mutane akalla miliyan 200 da ƙabilu 371, ta shafe tsawon lokaci bayan samun ƴanci daga turawa tana kokarin gina kanta, ta shiga jerin kasashe masu tasowa.

Yancin Naheriya.
Muhimman abubuwan tunawa a ranar da Najeriya ta samu ƴanci Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Najeriya ta yi bikin zagayowar ranar samun ƴanci karo na 64 ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, 2024 duk da halin ƙuncin da ake ciki.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi kai tsaye da safiyar Talata, inda ya yi waiwaye kan wasu abubuwan da suna faru tare da jaddada manufofinsa na gaba.

Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwa uku da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴanci, 1 ga watan Oktoba, 1960 wanda da wuya a manta da su.

1. Jawabin Sarauniya watau Queen Elizabeth II

Daya daga cikin abubuwan da ba za a manta da su ba da suka tabbatar da samun ‘yancin kan Najeriya shi ne jawabin Queen Elizabeth II.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 7 daga jawabin Tinubu na ranar samun 'yanci

A wajen bikin da aka gudanar a ɗakin taro na Royal Pavilion a filin Racecourse da ke Legas, Gimbiya Alexandra ta kasar Birtaniya ce ta karanta sakon Queen Elizabeth II a lokacin jawabinta.

A wani hoto da AP Newsroom ta ɗauka a ranar, an ga firaministan Najeriya Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa a zaune a gefen hagu a lokacin jawabin sarauniya.

Da take taya ‘yan Najeriya murnar samun ‘yanci tare da nuna kwarin gwiwa game da makomar kasar, Queen Elizabeth II ta ce Najeriya tana da gurbi na musamman a zuciyarta.

2. Sauke tutar Burtaniya

Daily Trust ta ruwaito cewa an sauke tutar ƙasar Burtaniya ne da tsakar dare a ranar 1 ga Oktoba, 1960, kuma aka daga tutar Najeriya a karon farko.

Wannan lokaci mai cike da tarihi ya kawo karshen mulkin Burtaniya da kuma farkon buɗe sabon shafi a Najeriya.

An tattaro cewa bikin kaddamar da tutar Najeriya da aka yi a Legas ya samu halartar dubban mutane, ciki har da manyan baki daga sassan duniya.

Kara karanta wannan

Ranar ƴanci: Shugaba Tinubu ya yi magana kan farashin kayan abinci, ya faɗi mafita

3. Jawabin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa

Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa ya gabatar da jawabi na musamman ga al'ummar kasar a wajen bikin kafa tutar Najeriya karon farko a tarihi.

Ya sha alwashin gina ƙasa, hadin kai da dimokuradiyya, ya kuma yi kira ga daukacin ƴan Najeriya su yi aiki tare da juna domin samun kyakkyawar makoma.

Jawabin da Abubakar Tafawa Ɓalewa ya yi a wannan lokaci ya shiga zuƙatan ƴan ƙasa, inda dandazon mutanen da suka halarci taron suka rika tafa masa.

Ranar ƴanci: Tinubu ya bada lambobin yabo

A wani rahoton kuma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da lambobin yabo na ƙasa domin murnar cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai

Shugaba Tinubu ya karrama shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da lambar yabo ta ƙasa ta GCON a ranar 1 ga Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262