Murnar 'Yancin Kai: Muhimman Abubuwa 6 da Za a Tuna da Su daga Jawabin Tinubu

Murnar 'Yancin Kai: Muhimman Abubuwa 6 da Za a Tuna da Su daga Jawabin Tinubu

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga ƴan Najeriya domin murnar zagayowar ranar da ƙasar nan ta samu ƴancin kai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaba Tinubu ya gabatar da jawabin ne a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024 domin murnar cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai.

Tinubu ya yiwa 'yan Najeriya jawabi
Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najeriya a.ranar Talata Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

Jawabin na Shugaba Tinubu ya taɓo batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ƙasar nan da faɗin tashin da magabata suka yi domin samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka.

Hadimin shugaban ƙasa, Dada Olusegun ya wallafa jawabin Tinubu a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Garambawul: An bukaci Tinubu ya nada El Rufai da wasu mutum 4 ministoci

Abubuwan tunawa daga jawabin Tinubu

Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin watanni 16 da ta yi a kan karagar mulki.

Jawabin shugaban ƙasan ya kuma ba da tabbaci ga ƴan Najeriya cewa abubuwa za su gyaru a ƙasar nan saboda matakan da aka ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ga wasu daga cikin abubuwan da za a tuna da su daga jawabin na shugaban ƙasan:

1. Farfaɗo da tattalin arziƙi

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a cikin jawabin na sa ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakan farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya samu ƙasar nan a wani yanayin da ba shi da wani zaɓi face ɗaukar matakai masu tsauri domin farfaɗo da tattalin arziƙi.

2. Nasarori a fannin tsaro

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa jami'an tsaron Najeriya sun samu nasarori a yaƙin da suke yi da ƴan ta'addan Boko Haram da ƴan bindiga a sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa a cikin shekara ɗaya ta kashe kwamandojin ƴan ta'addan Boko Haram da ƴan bindiga cikin sauri fiye da yadda aka taɓa yi a baya.

Ya bayyana cewa an kashe kwamandojin ƴan ta'adda da ƴan bindiga sama da 300 a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da wasu sassan ƙasar nan.

3. Sauƙaƙa tsadar rayuwa

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa yana sane da halin da ake ciki kan wahalar da ake sha musamman ta fannin tsadar abinci.

Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai domin ganin cewa an samu sauƙin rayuwa a ƙasar nan.

4. Inganta rayuwar matasa

Shugaba Tinubu ya sanar da cewa za a gudanar da taron matasa na kwanaki 30 domin tattaunawa kan matsaloli da ƙalubalen da suke fuskanta.

Ya ce taron zai samar da mafita kan matsalolin da matasa ke fuskanta a ɓangaren ilmi, samun aikin yi, ƙirƙire-ƙirƙire da tsaro.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Tinubu ya ba Akpabio, Barau da wasu mutum 3 lambar yabo ta kasa

Gwamnati na ci gaba da ba da rancen kuɗi ga ɗalibai yayin da aka samar da shirin 3MTT domin samar da ƙwararrun matasa a fannin fasaha.

5. Samar da ayyuka miliyan 2.5

A jawabin na sa ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da shirin The Renewed Hope Labour Empowerment Programme (LEEP) a ƙarƙashin ma'aikatar ƙwadago da samar da ayyukan yi.

Ya bayyana cewa shirin zai riƙa samar da ayyukan yi 2.5m a shekara wanda adadin hakan zai riƙa ƙaruwa.

6. Ba da lambobin yabo na ƙasa

Tinubu ya karrama shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da alƙalin alƙalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun da lambobin yabo na ƙasa na GCON.

Ya kuma ba mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas da lambobin yabo na ƙasa na CFR.

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya samu lambar yabo ta ƙasa ta CON.

Kara karanta wannan

Ranar ƴanci: Shugaba Tinubu ya yi magana kan farashin kayan abinci, ya faɗi mafita

Tinubu ya ba ƴan Najeriya haƙuri

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara lallashin ƴan Najeriya, ya ce nan ba da jimawa ba wahala za ta wanye kuma za su samu walwala da jin daɗi.

Bola Tinubu ya kuma buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kai wuri guda, kana su jajirce wajen gina ƙasar da kowa ke buri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng