Halin da Ake Ciki a Kaduna bayan Matasa Sun Fito Zanga Zanga a Wasu Sassan Najeriya

Halin da Ake Ciki a Kaduna bayan Matasa Sun Fito Zanga Zanga a Wasu Sassan Najeriya

  • An ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum yadda aka saba a jihar Kaduna a ranar, Talata 1 ga watan Oktoban 2024
  • Mutanen Kaduna sun ƙauracewa shiga zanga-zangar #October1Fearless da aka shirya gudanarwa a ranar murnar samun ƴancin kai
  • Mutane sun ci gaba da harkokinsu yadda suka saba yayin da aka jibge jami'an tsaro a wurare masu muhimmanci domin zama a cikin shiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Al'ummar jihar Kaduna sun ƙauracewa fitowa zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar, 1 ga watan Oktoban 2024.

Mutanen Kaduna sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum inda suka ƙi nuna sha'awar gudanar da zanga-zangar ta #October1Fearless.

Kara karanta wannan

Wasu miyagu sun buɗe wuta a kusa da gidan Ministan Tinubu, sahihan bayanai sun fito

Mutanen Kaduna sun ki fitowa zanga zanga
Mutane ba su fito zanga zanga a Kaduna ba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zanga-zanga: Halin da ake ciki a Kaduna

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an buɗe wuraren harkokin kasuwanci a cikin birni da kewaye, kuma shaguna a babbar kasuwar Sheikh Abubakar Gumi sun ci gaba da harkokin cinikayyarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mazauna birnin Kaduna sun gudanar da bukukuwan ranar samun ƴancin kai, yayin da wasu kuma suka ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai, an tura jami’an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda, jami’an tsaron farin kaya (DSS) da na hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) zuwa wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.

An jibge jami'an tsaron ne a wurare kamar Narayi High Cost, Barnawa, da shatale-talen filin wasa na Ahmadu Bello a matsayin matakan taka tsantsan.

Muhammad Najib ya shaidawa Legit Hausa cewa ko kaɗan mutane ba su damu da zanga-zangar ba domin halin ƙuncin da ake ciki ya yi musu yawa.

Kara karanta wannan

Rivers: Zanga zanga ta barke ana tsaka da gudanar da zabe, an gano dalili

"Mutane ba su fito ba suna ta gudanar da harkokinsu, ta yaya za ka fito zanga-zanga bayan kana tunanin abin da za ka samu ka sanya a bakinka?"

- Muhammad Najib

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Gwamna ya ba da shawara kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri, ta yi kira ga al'umma su guji shiga zanga-zangar da aka shirya ranar, 1 ga watan Oktoban 2024.

Gwamnatin ta buƙaci al'ummar jihar musamman matasa da ka da su shiga zanga-zangar wacce aka shirya gudanarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng