Kungiyoyi a Kaduna Sun Barranta da Zanga Zangar 1 ga Watan Oktoba

Kungiyoyi a Kaduna Sun Barranta da Zanga Zangar 1 ga Watan Oktoba

  • Gamayyar kungiyar matasan kasar nan sun barranta kansu da shiga zanga-zangar adawa da manufofin Bola Tinubu
  • Batun na zuwa ne a lokacin da wasu yan kasar nan ke fushi da yadda gwamnatin tarayya ke jagorancin kasar nan
  • Gamayyar kungiyar, ta ce gwamnatin kasar nan na fafutukar taimakawa jama'ar kasar nan ta hanyoyi da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Gamayyar kungiyoyin fararen hula a Kaduna ta tsame kanta daga zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin kasar nan yayin da ta cika shekara 64 da samun yanci.

Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu kungiyoyin su ka bayyana goyon bayan fitowa titunan kasar nan domin jawo hankalin gwamnati kan halin da su ke ciki.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

Tinubu
Matasan Kaduna sun ce babu su a zanga zangar adawa da Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na gamayyar, Kwamred Yusuf Lawal ne ya sanar da manema labarai cewa ba da su za a yi zanga-zanga ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kin shigar kungiyoyi zanga zanga

Jaridar Punch ta wallafa cewa gamayyar kungiyoyin ta ce ba za ta shiga zanga-zanga ba domin ta na ganin kokarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wajen inganta kasa.

Jami'in hulda da jama'a na gamayyar, Kwamred Yusuf Salisu ya bayyana cewa ranar 1 Oktoba, rana ce ta murna da mutunta sadaukarwar da magabatan kasar nan su ka yi.

Kungiyar matasa sun yabi gwamnatin Tinubu

Gamayyar kungiyar matasa ta yaba da yadda gwamnatin Bola Tinubu wajen kokarin inganta rayuwar matasa ta hanyar samar da ayyukan hannu.

Ya bayyana cewa a maimakon a shiga zanga-zanga, kamata ya yi gamayyar ta shawarci jama'a su rika bibiyar shugabannin kananan hukumominsu domin aikin cigaba.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: An gano illolin talauci, kungiya ta kawowa Tinubu shawara

Wasu matasa za su shiga zanga zanga

A baya mun ruwaito cewa wasu matasan Arewa, karkashin kungiyar Northern Youth Council of Nigeria sun bayyana goyon bayan zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya.

Sun bayyana cewa za su tattara kawunan matasan kasar nan wajen, musamman na Arewacin kasar nan domin a fito nuna rashin jin dadin wahalar da ake sha a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.