Murnar Samun 'Yancin Kai: Tinubu Zai Yi Jawabi ga 'Yan Najeriya, an Samu Bayanai

Murnar Samun 'Yancin Kai: Tinubu Zai Yi Jawabi ga 'Yan Najeriya, an Samu Bayanai

  • Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan murnar cika shekara 64 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024 a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin
  • A wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, ya ce shugaban ƙasan zai yi jawabin ne da safe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024.

Shugaban ƙasan zai yi jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe a wani ɓangare na bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun kai farmaki sansanin 'yan ta'adda, sun sheke miyagu masu yawa

Tinubu zai yiwa 'yan Najeriya jawabi
Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya ranar Talata Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa a shafinsa na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jawabin wani ɓangare ne na bukukuwan murnar cika shekara 64 da samun ƴancin kan Najeriya daga Turawan mulkin mallaka.

"An buƙaci gidajen talabijin, gidajen rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai na zamani da su kama tashar gidan talabijin ta Najeriya (NTA) da kuma gidan rediyon tarayyar Najeriya (FRCN) domin jawabin."

- Bayo Onanuga

Lokaci na ƙarshe da shugaba Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya shi ne yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agusta.

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Kara karanta wannan

Ranar ƴanci: Shugaban majalisar dattawa ya ƙara ba ƴan Najeriya hakuri, ya masu albishir

Gwamnati ta ba da hutun bikin 'yancin kai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin murnar zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng