Yan Bindiga Sun yi Gunduwa Gunduwa da Dan Gudun Hijira a Gaban Matarsa
- Al'umma a jihar Benue da ke Arewacin Najeriya sun shiga tashin hankali yayin da wasu yan bindiga suka yi mummunan ta'addanci
- An ruwaito cewa yan bindigar sun kewaye wani dan gudun hijira ne a gonarsa da bindigogi da adduna suka yi masa kisan gilla
- Wani tsohon ma'aikaci a sansanin yan gudun hijira ya bayyanawa manema labarai halin da ake ciki game da kisan da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Wasu yan bindiga sun yi kisan gilla ga wani dan gudun hijira mai suna Tali Tyosoo mai shekaru 45.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun kewaye dan gudun hijirar ne tare da matarsa yayin da suke aiki a wata gona.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Tali Tyosoo ya nemi mafaka ne a sansanin yan gudun hijira bayan yan ta'adda sun wargaza garinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi kisan gilla ga dan gudun hijira
Rahotanni da suka fito daga jihar Benue na nuni da cewa wani gungun yan bindiga sun kashe wani dan gudun hijira a yana aiki a gona.
Dan gudun hijirar mai suna Tali Tyosoo ya hadu da miyagun yan bindigar ne a ranar Lahadi da misalin karfe 2:00 na rana.
Yadda aka yanka dan gudun hijira
Matar Tali Tyosoo ta bayyana cewa suna cikin aiki ne sai ga yan bindiga su 10 dauke da bindigogi da arduna.
Suna isowa kuma suka bi mijinta da gudu yayin da ya fadi kasa sai suka fara sara shi da adda har sai da ya mutu.
An ajiye gawar dan gudun hijira
Wani tsohon manaja a sansanin yan gudun hijirar ya ce a yanzu haka an ajiye gawar marigayi Tali Tyosoo a sansanin da ilayansa suke.
Ibaah Jacob ya bayyana cewa Tali Tyosoo ya fara noma a kusa da sansanin ne domin ya samu damar ciyar da iyalansa yadda ya kamata.
Yan bindiga sun kashe dan siyasa
A wani rahoton, kun ji cewa miyagun yan bindiga sun kashe dan takarar kansila a jihar Kaduna tare da kaninsa a hanyarsu ta komawa gida.
Ana zargin harin ba ya rasa nasaba da siyasa, domin ya na dawowa daga yawon yakin neman zabe ne yan bindigar suka afka masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng