Matawalle: EFCC Ta Tabo Batun Bincikar Tsohon Gwamnan Zamfara

Matawalle: EFCC Ta Tabo Batun Bincikar Tsohon Gwamnan Zamfara

  • Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana cewa za ta yi bincike kan zargin da ake yiwa Bello Matawalle
  • EFCC ta bayyana cewa za ta binciki zargin da ake yiwa tsohon gwamnan na Zamfara kan karkatar da kuɗaɗen jihar
  • Wasu ƴan jam'iyyar APC ne dai suka garzaya hedkwatar hukumar domin neman ta ci gaba da bincikar ƙaramin ministan na tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta yi magana kan zargin karkatar da kuɗaɗen Zamfara da ake yiwa Bello Matawalle.

Hukumar EFCC ta ba da tabbacin cewa za ta gudanar da bincike kan tsohon gwamnan na jihar Zamfara, kan zargin almubazzaranci da kuɗaɗe a lokacin da yake kan mulki.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Zanga zangar da ake shrin yi ta gamu da tangarɗa a Kaduna

EFCC ta yi magana kan binciken Matawalle
EFCC ta ce za ta binciki zargin da ake kan Matawalle Hoto: @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele Oyewale ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar masu zanga-zangar neman a binciki Matawalle a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Me EFCC ta ce kan bincikar Matawalle?

Kakakin ya bayyana cewa hukumar za ta yi duk abin da za ta iya domin gudanar da bincike kan wannan zargin da ake yiwa tsohon gwamnan.

"Hukumar EFCC za ta yi duk abin da za ta iya bisa ikonta domin bincikar duk wani laifi na almundahanar kuɗi. Muna yin haka, kuma za mu ci gaba da yin hakan."
"Ina kuma so na yi amfani da wannan damar domin bayyana cewa EFCC ta amince da ƴancin ƴan Najeriya na gudanar da zanga-zangar lumana. Za mu isar da wannan sako ga shugaban hukumar, kuma za a ɗauki matakin da ya dace."

Kara karanta wannan

Hada baki da 'yan bindiga: Hukumar NSCDC ta dauki mataki kan jami'inta

- Dele Oyewale

Masu zanga-zangar ƙarƙashin ƙungiyar APC Akida sun taru ne a hedkwatar EFCC domin shigar da ƙorafi inda suka bukaci hukumar da ta ci gaba da binciken Matawalle wanda a halin yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro.

Batun shari'ar Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar masu kishin jihar Zamfara sun karyata labarin fara zaman kotu kan zargin tsohon gwamnan jihar, Dr. Bello Matawalle da alaka da ta'addanci.

Shugaban ƙungiyar masu kishin Zamfara, Yusuf Sani da Sakatare Dahiru Nasiru, sun ce karya ake yadawa kan shari'a da Dr. Matawalle.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng