1 ga Oktoba: Zanga Zangar da Ake Shrin Yi Ta Gamu da Tangarɗa a Kaduna

1 ga Oktoba: Zanga Zangar da Ake Shrin Yi Ta Gamu da Tangarɗa a Kaduna

  • Zanga-zangar da ake shirin yi ranar 1 ga watan Oktoba ta gamu da cikas, wata ƙungiya ta roki ƴan Kaduna su canza tunani
  • Mai magana da yawun ƙungiyar CCC reshen Kaduna, Yusuf Lawal ya ce zanga-zangar ba ta da amfani duba da abin da ya faru a baya
  • Ya buƙaci mutanen Kaduna su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, su ƙauracewa fita zanga-zangar gobe Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Wata ƙungiyar matasa a Kaduna (CCC) ta yi kira ga al'ummar jihar su nesanta kansu daga shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.

A cewar ƙungiyar, zanga-zangar da aka yi a watan Agusta ba ta haifar da komai ba sai asarar rayuka da dukiyoyi a sassa daban-daban.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta gargaɗi mutanen Kano kan zanga zangar da ake shirin yi

Taswirar Kaduna.
Wata kunguya ta roki mazauna Kaduna su kaucewa shiga zanga-zangar 1 ga watan Octoba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mai magana da yawun ƙungiyar, Kwamared Yusuf Lawal ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Litinin a Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun faɗi mafita madadin zanga-zanga

Ya buƙaci matasan jihar Kaduna su nemi zama da gwamnati domin tattaunawa da lalubo mafita kan tsananin da ake ciki maimakon ɓarna da sunan zanga-zanga.

Yusuf Lawal ya ce duk da ba za a rasa inda gwamnati mai ci ta yi kuskure ba amma akawai bukatar a ba ta lokaci domin ta cika alƙawurran da ta ɗauka.

"Zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan musamman ta EndBadGovernance, ta jawo barna mai yawa da kuma asarar rayuka, ciki har da mutuwar wani matashi a Zariya."
"Kowa ya san halin da ake ciki na matsin tattalin arziki amma kamata ya yi 1 ga watan Oktoba ta zama ranar murna da girmama gudummuwar da mazan jiya suka bayar.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Kungiyoyin Arewa sun amsa kiran fitowa tituna a ranar 1 ga Oktoba

"Rana ce ta tuna tarihi da haɗin kanmu a matsayin ƙasa guda, ba wai mu koma muna lalata kadarorin gwammati da na ƴan uwanmu da sunan zanga-zanga ba.

- In ji Kwamared Yusuf Lawal.

Matasan Kaduna sun ce babu amfanin zanga-zanga

Yusuf ya buƙaci mazauna Kaduna da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun maimakon shiga zanga-zangar da za ta iya haifar da hargitsi da tashin hankali.

A cewarsa, zanga-zanga ta gaza warware kalubalen da al'umma ke ciki, inda ya ƙara da cewa tattaunawa da ba gwamnati haɗin kai ya fi zama mafita a halin yanzu, in ji Vanguard.

Akpabio ya ƙara ba ƴan Najeriya haƙuri

A wani rahoton kuma Sanata Godswill Akpabio ya ƙara bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki na ƙunci da yunwa a faɗin ƙasar.

Shugaban majalisar dattawa ya tabbatar da cewa nan gaba kaɗan komai zai wuce kuma mutane za su shiga cikin haske da walwala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262