Gwamna Abba Ya Gano Matsalolin da Suka Hana Najeriya Samun Ci Gaba
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koka kan yadda Najeriya ta kasa samun ci gaban da ya kamata
- Abba ya bayyana cewa rashin shugabanci nagari, cin hanci da rashawa a matsayin abubuwan da ke kawo cikas
- Ya nuna cewa akwai buƙatar a haɗa kai wajen kishin ƙasa, aiki tuƙuru domin kawo ci gaba a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan abubuwan da suke kawo cikas ga ci gaban Najeriya.
Gwamna Abba ya bayyana raunin cibiyoyi, cin hanci da rashawa, rashin shugabanci nagari a matakin ƙasa da jiha da ƙananan hukumomi a matsayin abubuwan da ke kawo tasgaro ga ci gaban Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a wajen wata lacca da aka shirya domin bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya magantu kan matsalolin Najeriya
A jawabin da ya gabatar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan irin ci gaban da aka samu a tafiyar dimokuradiyyar ƙasar nan.
A cikin jawabin da ya yi, Gwamna Abba ya yi tambayoyi kan ko an cika manufofin dimokuraɗiyya na ƴanci, adalci da daidaito.
"Kamar yadda yake a ko na a duniya, nasarar dimokuradiyyar Najeriya tana da nasaba da ingancin shugabanci."
"A matsayinta na ƙasa mai tasowa mai tsarin siyasa mai sarƙaƙiya, ƙalubalen shugabanci da suka haɗa da cin hanci, cibiyoyi masu rauni da rashin gaskiya sun kawo cikas wajen ci gaban ƙasa."
"Dole ne mu gane cewa dimokuradiyya tafiya ce, kuma nasarar wannan tafiya ta dogara ne kan ingancin shugabanci a kowane mataki, ƙasa, jiha, da ƙananan hukumomi."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya yi kira da a haɗa kai wajen kishin ƙasa, aiki tukuru, da sadaukar da kai domin kawo ci gaba a ƙasar nan.
NNPP da Abba sun samu ƙaruwa a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya karbi tubabbun yan siyasa daga jam’iyyun adawa guda biyu, inda su ka yi sauyin sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Wasu daga cikin ƴaƴan ZLP da NRM ne su ka yanke shawarar ficewa daga cikin jam’iyyunsu bisa mabambantan dalilai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng