Zanga Zanga: Kungiyoyin Arewa Sun Amsa Kiran Fitowa Tituna a Ranar 1 ga Oktoba
- Matasan Arewacin kasar nan sun sun shirya shiga zanga zangar adawa da wahalar rayuwa a ranar 1 Oktoba
- Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta yi bikin cika shekara 64 da samun yanci daga turawan Birtaniya
- Daraktan hulda da jama'a na kungiyar Northern Youth Council of Nigeria ya ce su na tattara kan matasa kan zanga zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kungiyar matasa a Arewacin kasar nan ta Northern Youth Council of Nigeria (NYCN), ta fara tattaro kan sauran matasa gabanin zanga-zangar 1 Oktoba.
Matasan kasar nan sun ce za su fito a ranar da Najeriya ta cika shekaru 64 da samun yancin kai domin nuna bacin ransu kan tsananin da jama'a ke ciki.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa daraktan hulda da jama'a na NYCN, Hussaini Shu'aibu ne a tabbatar da haka a sanarwar da ya fitar a jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa za su gudanar da zanga zanga
Jaridar Independent ta wallafa cewa kungiyar NYCN ta ce dokar kasa ta ba kowa damar ya bayyana ra'ayinsa da hulda da fita zanga zangar nuna rashin jin dadinsu.
A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta jaddada aniyarta na fita zanga-zanga domin tunatar da gwamnati ta waiwayi halin da kasa ke ciki.
Dalilin zanga zanga kan manufofin gwamnati
Daraktan hulda da jama'a na NYCN, Hussaini Shu'aibu ya ce dokar kasar nan ta ba jama'a damar yin zanga zanga ne saboda jawo hankalin gwamnatin kan aikata ba dai-dai ba.
Ya ce zanga-zangar da aka gudanar a baya ta 1-10 Agusta, 2024 da wacce za a gudanar a gobe, manuniya ce kan rashin jin dadin yadda gwamnati ke tafiyar da kasa.
Matasa sun fara gangamin zanga zanga
A baya, mun ruwaito cewa matasan kasar nan sun fara gangamin fita zanga-zangar adawa da manufofin Bola Ahmed Tinubu da su ka ce sun jefa jama'a a cikin karuwar matsin rayuwa.
A taron da su ka gudanar da jihar Legas, matasan sun nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta rage farashin litar fetur da rage kudin wutar lantarki da yan kasar nan ke sha domin a samu sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng