Badakalar N27bn: EFCC Ta Sa Lokacin Gurfanar da Tsohon Gwamna a gaban Kotu
- Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shirya gurfanar da tsohon gwamnan jihar Taraba a gaban kotu
- Majiyoyi daga hukumar sun bayyana cewa za a gurfanar da Darius Ishaku a gaban kotu a ranar Litinin kan badaƙalar N27bn
- Jami'an hukumar EFCC dai sun cafke tsohon gwamnan ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) na iya gurfanar da tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a gaban kotu bisa zargin almundahanar N27bn a ranar Litinin.
Majiyoyi daga EFCC sun bayyana cewa Darius Ishaku, wanda ke da haƙƙin samun beli idan ya cika sharuɗɗan EFCC, zai gurfana a kotu ranar Litinin.
EFCC ta dade tana bibiyar Darius Ishaku
Jaridar Leadership ta ce majiyar ta ce hukumar ta EFCC ta shafe shekaru tana bin diddigin tsohon gwamnan kuma tana da tuhume-tuhume masu ƙarfi a kansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an hukumar EFCC sun cafke Darius Ishaku a ranar Juma’a a gidansa da ke Abuja.
Kakakin hukumar, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ƙi yarda ya yi ƙarin bayani a kai, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
Majiyoyi daga EFCC sun ce har yanzu tsohon gwamnan na hannun hukumar har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Me ake tuhumarsa a kai?
Majiyar ta ƙara da cewa an shigar da tuhume-tuhume aƙalla 15 a kan tsohon gwamnan kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu domin an tattara shaidu a kansa.
Darius Ishaku, wanda ya bar mulki a shekarar 2023 bayan ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas, an cafke shi a gidansa da ke Abuja da safiyar ranar Juma’a.
"Eh, yana hannunmu a yanzu. Tun bayan tafiyarsa a matsayin gwamnan jihar muna ta bincikensa a ɓoye. Ya yi ta’ammali da kuɗi masu yawa."
- Wata majiya
EFCC ta ƙalubalanci tsohon gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce a shirye ta ke wajen fuskantar tsohon gwamnan Kogi, Bello Yahaya a kotu.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar EFCC, Dele Oyewale ya ce dole sai Yahaya Bello ya fuskanci alƙali kan zargin da ake yi masa.
Asali: Legit.ng