Dauda Vs Matawalle: Kungiya Ta Goyi Bayan Gwamnan Zamfara, Ta Ba da Shawara

Dauda Vs Matawalle: Kungiya Ta Goyi Bayan Gwamnan Zamfara, Ta Ba da Shawara

  • Ƙungiyar Arewa Peace Foundation (APF) ta fito ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal
  • Ƙungiyar APF ta buƙaci masu sukar gwamnan da masu ruwa da tsaki su haɗa da kai da shi domim dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara
  • Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar APF wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ya kuma yaba da salon mulkim Gwamna Dauda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar Arewa Peace Foundation (APF) ta nuna goyon bayanta ga Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara.

Ƙungiyar APF ta buƙaci masu sukar gwamnan da masu ruwa da tsaki su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, su haɗa kai da shi wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya kan matsalar tsaro, ya ba da shawara

Kungiya ta goyi bayan Dauda Lawal
Kungiyar APF ta nuna goyon baya ga Gwamna Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Bello Abdulhamid, a wani taron manema labarai a Kaduna, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiya ta yabi Gwamna Dauda

Bello Abdulhamid ya yabawa jagorancin Gwamna Dauda Lawal, inda ya ce ya farfaɗo da Zamfara bayan shekaru da dama na tashin hankali da ƙalubalen tattalin arziƙi.

Ƙungiyar ta yabawa ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa noma da kiwo, magance matsalar ƴan bindiga da inganta ilimi.

Ƙungiyar APF ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da kalaman ƙin jinin gwamnati, inda a maimakon hakan su goyi bayan ƙoƙarin da Gwamna Dauda Lawal ke yi na kawo ci gaba a Zamfara.

Ƙungiyar ta jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin fitar da jihar daga ƙalubalen da take fuskanta da kuma samun ci gaba mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Matasan APC sun fadi ministan da ya kamata Tinubu ya dakatar, sun fadi dalili

Tsohon kwamishina ya caccaki Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya daina ɗora alhakin matsalar rashin tsaro kan Alhaji Bello Matawalle.

Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda ya buƙaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng