Murnar Samun 'Yan Cin Kai: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da hutu domin bikin murnar zagayowar da ƙasar nan ta samu ƴancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka
- Gwamnatin ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar cika shekara 64 da samun ƴancin kai
- Ministan harkokin cikin gida wanda ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya ya taya ƴan Najeriya murnar zagayowar lokacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin murnar zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai.
Gwamnatin tarayya ta ba da hutu
Babban sakatare a ma'aikatar cikin gida Dr Magdalene Ajani ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a shafin X na ma'aikatar harkokin cikin gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ayyana ranar hutun ne a madadin gwamnatin tarayya.
Ministan ya taya ƴan Najeriya na cikin gida da ƙasashen waje murnar zagoyawor lokacin.
Dr. Olabunmi Tunji-Ojo ya kuma yaba da haƙuri da jajircewar ƴan Najeriya, inda ya bayyana cewa sadaukarwar da suke yi ba za ta tafi a banza ba.
"Yayin da yake taya ƴan Najeriya murnar zagayowar ranar samun ƴancin kai, Dr. Olabunmi Tunji-Ojo ya buƙace da su ci gaba da jajircewa wajen gina ƙasa."
Dr. Magdalene Ajani
A ranar, 1 ga watan Oktoban 1960 ne dai Najeriya ta samu ƴancin kai daga hannun ƙasar Ingila.
Gwamnoni sun ba da hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatocin jihohin Legas, Osun, Oyo da Ogun sun ayyana Talata 20 ga watan Agusta a matsayin ranar hutu domin tunawa da Ranar Isese.
Bayanin ba da hutun na kunshe ne a cikin wasu sanarwa daban-daban da kwamishinonin yada labarai na kowace jiha suka fitar.
Ranar Isese tana nufin nau'ikan bukukuwan al'adun da Yarabawa ke gudanarwa a Najeriya da Cuba, Brazil, Amurka, Benin, da sauran ƙasashe
Asali: Legit.ng