"An Samu Canji": Hukumar Alhazai, NAHCON Ta Sanar da Sabon Tsarin Aikin Hajjin 2025
- NAHCON ta sanar da wani sabon tsari da hukumomin ƙasar Saudiyya suka kawo wanda za a fara aiwatarwa a hajjin 2025
- Mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Usara ta ce daga yanzu ciyarwa da ɗakunan kwanan alhazai sun koma hannun Saudiyya
- Ta ce tuni shirye-shiryen hajjin baɗi suka yi nisa kuma hukumar ta zauna da wakilan jihohi kan wannan sabon tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa watau NAHCON ta sanar da wasu canje-canje da aka samu a aikin hajjin da za a yi idan Allah ya kaimu baɗi 2025.
NAHCON ta bayyana cewa hukumomin kasar Saudiyya za su karɓi ragamar ciyarwa da ɗakunan kwanan alhazai a Makkah a Madinah.
Premium Times ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON ta fara shirin hajjin 2025
Fatima Usara ta ce an amince da sabon tsarin ne a yayin wani taro ta intanet tsakanin hukumar da ma'aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya (MoHU).
Ta kuma tabbatar da cewa shirye-shiryen hajjin 2025 sun yi nisa kuma hukumar ta zauna da shugabannin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi ranar 23 ga watan Satumba.
Fatima ta ce a wannan zama, kwamishinan sashin ayyuka na NAHCON, Anofi Olanrewaju-Elegushi ya sanar da jihohi tsarin da Saudiyya ta ɓullo da shi.
Saudiyya ta kawo sabon tsari a hajjin 2025
Kakakin NAHCON ta haƙaito kwamishinan na cewa kamafanonin kula da mahajjata da aka fi sani ma'assasa za su karɓi ragamar ciyarwa da ɗakunan kwanan alhazai a Makkah da Madinah.
A ruwayar Guardian, kwamishinan NAHCON ya ce:
"Wannan tsarin zai shafi kowace ƙasa za ta tura mutanenta hajji kuma za a fara aiwatar da shi ne daga alhazan baɗi 2025.
"Kun sani dai a baya ma'aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya MoHU ta gabatar da shawarar ɗaukar nauyin ciyarwa a Masha’ir a 2022, kuma a shekarar aka aiwatar."
EFCC ta saki tsohon shugaban NAHCON
A wani rahoton kuma hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayar da belin tsohon shugaban NAHCON da sakatarensa.
EFCC ta saki Jalal Arabi tare da Abdullahi Kontagora bayan sun cika sharuɗɗan belinsu a hannun hukumar yaki da rashin gaskiyar
Asali: Legit.ng