Sarkin Farko daga Kudancin Najeriya Ya Dura Maiduguri domin Jajen Ambaliyar Ruwa

Sarkin Farko daga Kudancin Najeriya Ya Dura Maiduguri domin Jajen Ambaliyar Ruwa

  • Sarki mai daraja ta daya a Kudancin Najeriya, Appolus Chu ya jagoranci tawaga zuwa jihar Borno domin jaje kan ambaliyar ruwa
  • Mai martaba Appolus Chu ya samu rakiyar yan fadarsa kuma mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar ya karbe su
  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya mika godiya ga sarkin bisa kokarin da ya yi wajen tunawa da mutanen Maiduguri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta karbi baƙuncin babban sarki a Kudancin Najeriya domin mata jaje kan ambaliyar ruwa.

An ruwaito cewa basarake mai mulkar masarautar Eleme a jihar Rivers, Appolus Chu ne ya kai ziyara jihar Borno.

Kara karanta wannan

Dorinar Ruwa ta yi ajalin dogarin Sarki, Gwamna ya kadu

Appolus Chu
Sarki daga Kudu ya je jaje Maiduguri. Hoto: @AppolusChu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sarkin ya dauki tawaga ce mai karfi daga fadarsa domin jaje ga al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki daga Kudu ya je jaje a Maiduguri

Jihar Borno ta karbi baƙuncin mai martaba sarkin jihar Rivers, Appolus Chu bayan ambaliyar ruwa.

Ana ganin ziyarar za ta kara karfafa alakar sarakunan Arewacin Najeriya da Kudu musamman a lokutan jarrabawa.

Sarki Chu ya gana da Shehun Borno

Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi ya tarbi sarki Appolus Chu a fadarsa.

Jaridar This Day ta wallafa cewa Shehun Borno ya mika godiya ga sarki Appolus Chu inda ya ce alaƙarsu za ta cigaba da kasancewa har abada.

Sarki ya yi jaje ga gwamna Zulum

A daya bangaren, sarki Appolus Chu ya gana da gwamna Babagana Umara Zulum inda ya masa jaje kan ambaliyar ruwan Maiduguri.

Kara karanta wannan

Maiduguri: Gwamna ya dura Borno, ya ƙara jika waɗanda ambaliya ta shafa da miliyoyi

Gwamna Babagana Umara Zulum ya mika godiya ga sarkin inda ya ce zai cigaba da ƙoƙarin ganin al'ummar Borno sun samu sauki.

NDLEA ta kama rubabben abinci a Maiduguri

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NDLEA ta kai samame kasuwannin Maiduguri domin tabbatar da ingancin abinci da magani da ake sayarwa bayan ambaliya.

NDLEA ta ce an samu wasu masu sayar da magani da suka rika sayar da ruɓaɓɓun magunguna ga al'ummar jihar kafin daukar mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng