Ministan Tinubu Ya Shiga Matsala, An Yi Wa Layin Wayarsa Kutse a Najeriya

Ministan Tinubu Ya Shiga Matsala, An Yi Wa Layin Wayarsa Kutse a Najeriya

  • Ministan ilimi na tarayya, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa an yi kutse a layin wayar da yake Whatsapp da shi
  • A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ilimi ta yi kira ga ƴan Najeriya su guji duk wani sako da aka turo masu da lambar
  • Ta ce yanzu haka dai an sanar da hukumomin da ya dace kuma sun fara ɗaukar mataki domin a iya shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu da ba a sani ba sun yi kutse a layin wayar salular ministan ilimi na ƙasa, Farfesa Tahir Mamman.

Ministan ya gargaɗi ƴan Najeriya da su guji kira ko saƙonni ta lambar wayar da aka yi wa kutse domin kaucewa ƴan damfara.

Kara karanta wannan

'Zai kara aure?': Al'umma sun bayyana ra'ayoyi kan sakin Seaman Abbas

Farfesa Tahir Mamman.
Ministan Ilimi ya tabbatar da sn yi wa layin wayarsa kutse Hoto: @ProfTahirMamman
Asali: Twitter

Ministan Ilimi ya tabbatar da kutsen

Farfesa Tahir Mamman shi ne ya sanar da haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na manhajar X jiya Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce:

"An yi wa layin wayata kutse, ina fatan mutane za su daina kiran layin kuma ku yi watsi da duk wani saƙo da aka turo na neman kudi har sai an warware matsalar, Na gode.

Yadda aka yiwa ministan ilimi kutse

Ma'aikatar ilimi ta tabbatar da labarin kutsen wayar ministan a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Boriowo Folasade ya fitar yau Jumu'a.

Ya ce a halin yanzu wasu tsagerun ƴan kutse da ba a san ko su waye ba, su ke amfanin da layin wayar.

"Ofishin ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman na sanar da jama'a cewa an yi kutse a lambar da ministan ke WhatsApp da ita kuma yanzu wasu mutane ke amfani da ita.

Kara karanta wannan

Talauci: Gwamnati ta kara ba yan kasa hakuri, Minista ya ce sauki na tafe

"Ba mu ji daɗin abin da ya faru ba kuma muna kira ga jama'a su yi fatali da saƙonnin neman agaji ko kuɗi da wannan lambar ta aiko masu," in ji sanarwar.

Folasade ya ƙara da cewa a halin yanzu an sanar da hukumomin da ya dace domin ɗaukar mataki.

Gwamnatin Tarayya ta musanta ƙayyade shekarun SSCE

A wani rahoton kuma gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan batun mafi karancin shekarun zana jarabawar fita sakandire WAEC, NECO da NABTEB.

Ƙaramin ministan ilimi, Dr Tanko Sununu ya ce jarabawar share fagen shiga jami'o'i ce aka sanya wa dokar cika shekara 18.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262