Gwamna Ya Yi Magana Bayan Mai Ɗakinsa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Asibiti

Gwamna Ya Yi Magana Bayan Mai Ɗakinsa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Asibiti

  • Gwamnan Akwa Ibom, Umo Edo ya yi godiya ga dukkan masu fatan alheri da alhinin rasuwar matarsa Patience Edo
  • Eno ya yi godiya ne a lokacin da yake magana kan mutuwar mai ɗakinsa bayan fama da jinya ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba
  • A wata sanarwa da gwamnatin Akwa Ibom ta fitar, gwamnan ya ce rashin ba zai hana shi ci gaba da kokarin sauke nauyin al'umma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno ya yi magana sa'o'i kaɗan bayan sanar da mutuwar matarsa da safiyar ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba, 2024.

A wata sanarwa da gwamnatin Akwa Ibom ta fitar, Misis Patience Umo Eno ta cika ne ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba a Asibiti bayan fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu, gwamnoni sun yi ta'aziyyar uwar gidan gwamnan Akwa Ibom

Gwamna Umo Edo da marigayiya Patience.
Gwamnan Akwa Ibom ya miƙa godiya ga masu ta'aziyya da fatan alheri bayan rasuwar matarsa Hoto: @PstPatienceEno
Asali: Twitter

Sai dai sanarwar da gwamnatin ta wallafa a manhajar X, ba ta bayyana wane irin ciwo ne ya yi ajalin uwargidar gwamnan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya godewa masu fatan alheri

Gwamna Eno ya godewa masu ta'aziyya da fatan alheri ga iyalansa, inda ya tabbatar da cewa lamarin ba zai shafi harkokin tafiyar da gwamnatinsa ba.

Sanarwar ta ce:

"Mai Girma Gwamna Fasto Umo Eno na godiya ga duk wanda ya taya iyalansa alhini a wannan hali kuma yana tabbatarwa mazaunan Akwa Ibom cewa duk da wannan rashi, ba abin da zai taɓa harkokin gwamnati."

A sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Ini Ememobong, iyalan gwamnan sun bukaci a bar su su ɗan keɓe a daidai lokacin da suke jimami.

Tuni da ƴan uwa da abokan arziki da masu fatan alheri suka fara sakon ta'aziyya da alhini ga gwamnan da iyalansa bisa wannan rashi da suka yi.

Kara karanta wannan

Akwa Ibom: Muhimman abubuwa 5 kan matar gwamna da ta rasu

PDP ta dakatar da kamfe a Akwa Ibom

A wani rahoton na daban kun ji cewa mutuwar mai dakin mai girma gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Eno ta jefa mazauna jihar cikin alhini.

A sakon ta'aziyyarta ga gwamna Umo Eno, PDP a jihar ta yi addu'ar samun dangana ga iyalan marigayiyar, sanna ta dakatar da harkokin kamfe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262