Ganduje, Zababben Gwamnan Edo da Gwamnonin APC Sun Shiga Ganawa da Tinubu
- Bayan kammala zaben Edo, shugaban APC, Abdullahi Ganduje zai gabatar da zaɓaɓɓen gwamna, Monday Okpebholo
- Ganduje ya jagoranci gwamnonin APC zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024
- Daga cikin wadanda suke cikin tawagar sun hada da Sanata Adams Oshiomhole da mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya jagoranci gwamnonin APC zuwa fadar shugaban kasa.
Abdullahi Ganduje zai gabatar da zaɓaɓɓen gwamnan Edo, Monday Okpebholo ga Bola Tinubu a birnin Abuja.
Gwamnonin APC suna ganawa da Tinubu
Daily Trust ta ruwaito cewa Ganduje na tare da duka gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran gwamnonin sun hada Hope Uzodinma na jihar Imo da AbdulRazak AbdulRahman na Kwara.
Sai kuma Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da Usman Ododo na jihar Kogi da kuma Dapo Abiodun na Ogun.
Daga cikin tawagar akwai Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole da mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu.
Okpebholo ya lashe zaben gwamnan Edo
Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta sanar da dan takarar APC, Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo.
A yau Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024 hukumar INEC ta ba Okpebholo sakifiket domin tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe.
Dan takarar gwamnan na APC ya samu kuri'u har 291,667 yayin da mai bi masa daga jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 247,244.
Ana hasashen APC za ta lashe zaben jihohi
Kun ji cewa kafin zaben 2027, za a gudanar da zaben gwamnonin jihohi akalla hudu wanda ake ganin APC za ta iya samun nasara.
Jihohin sun hada da Ondo da Anambra da Osun da kuma Ekiti wanda aka sa ran jam'iyyar APC za ta takawa rawar gani.
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Edo inda Monday Okpebholo ya yi nasara.
Asali: Legit.ng