Ambaliya Ta Mamaye Makarantu da Asibitoci, Ruwa Ya Cinye Kauyuka 82

Ambaliya Ta Mamaye Makarantu da Asibitoci, Ruwa Ya Cinye Kauyuka 82

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Neja na nuni da cewa an samu mummunar ambaliyar ruwa da ta jawo asarar dukiya mai yawa
  • An ruwaito cewa ambaliyar ta shafi ƙauyuka kusan 100 inda mutane da dama suka rasa gidaje da wuraren da suke noma abincinsu
  • Haka zalika ambaliyar ta shafi makarantu da asibitoci a yankunan wanda hakan ke zama barazana ga lafiya da harkar Ilimi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Ana cigaba da samun mummunar ambaliyar ruwa a Arewacin Najeriya inda mutane ke tafka asarar dukiya.

An samu mummunar ambaliyar ruwa a jihar Neja inda mutane da dama suka rasa gidaje da gonaki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

Ambaliya
An yi ambaliya a Neja. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mummunar ambaliyar ta faru ne a ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya ta malale ƙauyuka a Neja

Rahotanni sun nuna cewa bayan ruwa da aka tafka, ambaliya ta mamaye kauyuka 51 a yankin Muregi.

Haka zalika mummunar ambaliyar ta mamaye kauyuka kimanin 31 a yankin Gbara na karamar hukumar Mokwa.

Wuraren da ambaliyar ta shafa sun hada da Egbagi-Majin Manna, Lugwa, Kpachita Wadata Edolusa, Esungi, Gbafu, Sanchiya, Kuchitagi, Badaifu, Tswasha, Jiffu, Nku kpata da Muregi.

Ruwa ya mamaye asibitoci da makarantu

An ruwaito cewa ruwan ya mamaye makarantu da asibitoci kimanin 90 a yankunan Muregi, Gbara da Ja'agi a karamar hukumar Mokwa.

Sai dai an ruwaito cewa duk da tsanani ambaliyar, ba a rasa rai ko daya ba kuma mutanen da abin ya shafa an samar musu da wurin zama.

Kara karanta wannan

Satar wayoyi 100 ta jefa wasu daliban Arewa a cikin matsala, 'yan sanda sun yi bayani

Wani jami'in gwamnatin jihar Neja, Habibu Abubakar Wushiwushi ya ce gwamnatin jihar ta yi jaje ga al'ummar tare da kira garesu da su kaucewa wurare da ake hasashen ambaliya.

An yi ambaliya a jihar Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa a Sokoto ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a jihar Kebbi.

Shugaban hukumar NEMA a Sokoto, Aliyu Shehu-Kafindagi ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wajen da aka yi ambaliyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng