Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Tsare Tsare Masu Zafi, Za a Fadada Kofofin Haraji

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Tsare Tsare Masu Zafi, Za a Fadada Kofofin Haraji

  • Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta fitar da sanarwa kan wasu tsare tsare da ta kawo a kan tattalin arzikin Najeriya
  • Hadimin shugaban kasa a kan tsare-tsaren haraji, Taiwo Oyedele ne ya fitar da sanarwar kan yadda sabon tsarin zai fara aiki
  • Taiwo Oyedele ya bayyana cewa za a gabatar da kudirin sabon tsarin a gaban majalisa domin tantancewa da tabbatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar wasu sababbin tsare tsare kan tattara haraji a kan yan kasa.

Shugaban kwamitin tattarawa da tsara haraji, Taiwo Oyedele ne ya fitar da sanarwa kan sabon tsarin gwamnatin.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

Shugaba Tinubu
Gwamnatin Tinubu ta kara kawo tsarin tattara haraji. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Legit ta gano yadda tsari zai gudana ne a cikin wani sako da Taiwo Oyedele ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu za ta fadada kofofin haraji

Taiwo Oyedele ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta amince da wasu tsare tsare da suka shafi haraji da tattali har 15.

Daga cikin tsare tsaren akwai shirin TICC da zai ba gwamnatin damar faɗaɗa kofofin haraji domin kara samun kudin shiga.

Sauran tsare tsaren harajin gwamanti

Jaridar Business Day ta wallafa cewa gwamnatin na shirin habaka tattali wajen amfani da tattalin arzikin yanar gizo domin samar da ayyuka da yaki da talauci.

Haka zalika akwai tsarin da zai rage tsadar kayayyaki da yan Najeriya ke fama da su a halin yanzu sai kuma kara kudin lamuni ga dalibai.

Gwamnatin tarayya za ta yi haɗaka da jihohi

Kara karanta wannan

N177.4bn: Shekarun rashin ruwa a Kano zai zo ƙarshe, gwamnati na aiki da kasar Turai

Gwamnatin tarayya ta kuma sanar da cewa za ta yi haɗaka da jihohi domin saukake haraji ga wasu nau'ukan kananan sana'o'i.

Cikin sana'o'in da za a saukakawa haraji akwai masu sayar da dabbobi da harajin da ake karba wajen masu shaguna a kasuwanni.

Bill Gates ya koka kan haraji a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa a kwanakin baya shahararren mai kudi a duniya, Bill Gates ya kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan muhimman abubuwa.

Bill Gates ya bayyana cewa kudin haraji da ake karba wajen yan Najeriya ya yi kadan kuma hakan ba zai kawo cigaba a kasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng