Kotu Ta Umarci a Kwace Kudin Najeriya a Amurka? Gwamnatin Tarayya Ta Yi Martani

Kotu Ta Umarci a Kwace Kudin Najeriya a Amurka? Gwamnatin Tarayya Ta Yi Martani

  • Antoni Janar na tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, ya musanta batun cewa wata kotu ta yi umarnin a ƙwace $21m na Najeriya da ke Amurka
  • Ministan na shari'a ya bayyana cewa ko kaɗan babu wata kotu a Amurka ta ba da umarnin ƙwace kuɗaɗen mallakin gwamnatin Najeriya
  • Ya ƙalulabanci kafafen yaɗa labaran da suka buga labarin da su wallafa kwafin umarnin kotun wanda ya ba da iznin ƙwace kuɗaɗen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Antoni Janar na tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, ya yi magana kan batun ƙwace kuɗaɗen Najeriya a Amurka.

Lateef Fagbemi ya bayyana cewa, babu wani lokaci da kotun ƙasar Amurka ta ba da izinin ƙwace wasu kuɗaɗe mallakar gwamnatin Najeriya a hannun JP Morgan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki manoma a gona, sun sace mutum 6

Gwamnatin Najeriya ta musanta kwace kudadenta a Amurka
Lateef Fagbemi ya musanta batun kwace kudaden Najeriya a Amurka Hoto: @FedMinOfJustice
Asali: Twitter

Kotu ta ce a karbe kudin Najeriya?

Jaridar Tribune ta ce ministan ya yi martanin ne bayan wata jarida ta yi iƙirarin cewa wata kotu a Amurka ta ba da umarnin ƙwace kuɗaɗen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wallafar da jaridar ta yi ta ce wata kotu a Birtaniya ta ba da iznin Williams Emovbira ya ƙwace $21m daga asusun CBN na JP Morgan a birnin New York.

Wane martani gwamnatin Najeriya ta yi?

A cewar Fagbemi, kotun ta Amurka ta ƙi kawai yarda da buƙatar Najeriya ne ta a yi fatali da ƙorafin saboda kariyar da take da ita a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya bayyana cewa abin da matakin da kotun ta ɗauka a ranar 12 ga watan Agustan 2024, yake nufi shi ne yanzu za a saurari ƙarar, inda kowane ɓangare zai gabatar da bayanansa kafin kotun ta yanke hukuncin ƙarshe.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin tarayya sabon wa'adi, ta kafa sharadi

"Babu ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labaran da suka buga labarin da suka nemi jin ta bakin gwamnatin Najeriya."
"Saboda haka muna ƙalubalantarsu da su wallafa kwafin umarnin kotun Amurka wanda ya ba da iznin ƙwace kuɗaɗen."
"Yana da kyau a bayyana cewa Najeriya ta ɗaukaka ƙara kan matakin da kotun ta ɗauka."

- Lateef Fagbemi

Kamfanin China na son zama da gwamnatin tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin kasar China mai suna Zhongshan ya bayyana cewa a shirye ya ke da ya tattauna da gwamnatin Najeriya wajen cimma matsaya.

Hakan na zuwa ne bayan wata kotu a Faransa ta yanke hukuncin gwamnatin Ogun ta biya kamfanin $74.5m bayan soke wata yarjejeniya da aka kulla.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng