Jami'an Tsaro Sun Kara Samun Nasara, Sun Hallaka Gawurtaccen Ɗan Bindiga a Zamfara

Jami'an Tsaro Sun Kara Samun Nasara, Sun Hallaka Gawurtaccen Ɗan Bindiga a Zamfara

  • Jami'an tsaro sun kara kashe wani hatsabibin ɗan bindiga, Kachalla Makore a jihar Zamfara da ke Arewa naso Yammacin Najeriya
  • Rahotanni sun ce an sheke Makore ne a hanyarsa ta zuwa ɗauko gawar Sani Black, da yan banga suka kashe a yankin Ɗan Sadau
  • Wannan nasara na zuwa a lokacin da rundunar tsaro ta lashi takobin kakkaɓe jagororin ƴan bindiga da suka hana mutane zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Jami'an tsaron Najeriya sun kara yin nasarar hallaka wani jagoran ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin kasar nan.

Gawurtaccen ɗan bindiga mai suna Kachalla Makore ya gamu da ajali ne a lokacin da ya jagoranci zuwa ɗauko gawar wanda ƴan banga suka kashe, Sani Black.

Kara karanta wannan

Dakaru sun kara yin gagarumar nasara, sojoji sun hallaka abokin Bello Turji

Taswirar Zamfara.
Jami'an tsaro sun ƙara kashe kwamandan ƴan bindiga, Kachalla Makore a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na manhajar X yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamfara: An kashe Makore da wasu yan bindiga

Ya ce jami'an tsaron sun hallaka Kachalla Makore tare da wasu ƴan bindiga da dama a kusa da titin Kwankele da ke yankin Magami a ƙaramar hukumar Gusau.

Rahotanni sun ce Kachalla Makore da wasu mayaƙansa sun fito ne da zummar zuwa ɗauko gawar Kachalla Sani Black, wanda ƴan banga suka sheke a yankin Ɗan Sadau.

Idan ba ku manta ba, sojoji sun hallaka Sani Black ne a kauyen Magama Mai Rake da ke ƙaramar hukumar Maru, ɗaya daga cikin fitattun sansanonin ƴan bindiga.

Yadda Kachalla Makore ya addabi mutane

Kachalla Makore ya zama kwamandan tawagar ƴan bindiga ne bayan mutuwar maigidansa, Kachalla Damuna.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Ɗan takarar PDP ya koka, ya hango wata matsala ana tsaka da zaɓe

Ya shahara da aikata miyagun laifuka a kusa da kauyen Kangon Garacci da ke yankin Dan Gulbi a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Wannan nasara ta sheke Kachalla Makore na zuwa ne a lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka kara zage dantse don kawo ƙarshen ta'addancin ƴan bindiga.

Sojoji, ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kara ƙaimi da nufin murkushe duk wasu ayyukan ta'addanci a shiyyar Arewa maso Yamma.

Sojoji sun sha alwashin kakkaɓe ƴan bindiga

A wani rahoton kuma bayan hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu, rundumar tsaro ta sha alwashin kawo karshen sauran yan bindiga.

Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce za su kawo karshen rikakken dan ta'adda, Bello Turji nan ba da jimawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262