Gwamna Zulum Ya Fara Rabawa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa Kuɗi da Kayan Abinci

Gwamna Zulum Ya Fara Rabawa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa Kuɗi da Kayan Abinci

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya kaddamar da fara rabon kayan tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna a jihar Borno
  • Zulum ya bayyana yadda aka raba mutanen da ibtila'in ambaliyar ya shafa rukuni rukuni gwargwadon asarar da kowane magidanci ya yi
  • Ya kuma miƙa godiya ga gwamnatin tarayya da sauran waɗanda suka tallafa da kudi ko kayan agaji domin ragewa al'umma raɗaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum, ya kaddamar da rabon kayan tallafi a hukumance ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

Ambaliyar da ta faru sakamakon kwararan ruwa daga madatsar ruwa ta Alau, ta lalata gidajen jama'a da dama da wasu ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

BUA: Mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri sun ƙara samun tallafin N2bn

Babagana Umaru Zulum.
Gwamna Zulum ya kaddamar da fara rabon kayan tallafi da kudi ga waɗanda ambaliya ta shafa Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Kamar yadda Leadership ta tattaro, ana tunanin ibtila'in ya shafi akalla mutane miliyan biyu a ciki da wajen Maiduguri, babban birjin jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya faɗi yadda rabon zai kasance

Da yake kaddamar da shirin a Maiduguri, Farfesa Zulum ya ce za a fara rabon kayan tallafin da magidanta 5,235 a Gwange 1 da ke ƙaramar hukumar birni.

A cewar Zulum, 587 daga cikin magidantan sun rasa gidajensu gaba daya yayin da 2,365 kuma ambaliya ta masu ɓarna kadan, sauran 2,283 kuma kaɗan ta shafe su.

Gwamnan ya ce kowane magidanci da ya samu ƙarancin ɓarna a gidansa za a ba shi tallafin N100,000 da muhimman kayayyaki kamar shinkafa, wake, tabarmi, barguna da gidan sauro.

Ya ce wadanda suka yi asara mai yawa kamar rushewar gidajensu, za a biya su diyya gwargwadon abin da suka rasa.

Kara karanta wannan

"Sama da mutum miliyan 88 na fama da talauci," Sheikh Pantami ya ba matasa mafita

Gwamna Zulum ya godewa waɗanda suka tallafa

Zulum ya yi godiya ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, hukumomin majalisar ɗinkin duniya, abokan hulɗa da daidaikun mutane bisa tallafin da suka bayar.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan Borno, Umar Usman Kadafur, da wasu manyan jami’an gwamnati, rahoton Punch.

Ambaliyar Maiduguri: BUA ya ba da tallafin N2bn

Mun kawo maku cewa Abdul Samad Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA Group ya ba waɗanda ambaliya ta rutsa da su a jihar Borno tallafin N2bn.

Babban daraktan kamfanin, Kabiru Rabiu ne ya sanar da haka yayin da tawagar BUA Group ta kai ziyarar jaje ga gwamnan jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262