Zanga Zangar Oktoba: Matasa Sun Fitar da Zafafan Bukatu 17 ga Tinubu

Zanga Zangar Oktoba: Matasa Sun Fitar da Zafafan Bukatu 17 ga Tinubu

Matasan Najeriya sun cigaba da shirye shiryen yin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Legit ta tattauna da wani matashi, Muhammad Sa'idu dommin jin ko zai shiga zanga zangar a wannan karon

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matasan Najeriya na cigaba da shirye shiryen gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu.

A wannan karon, matasan sun fitar da wasu jerin bukatu 17 domin gwamnatin tarayya ta cika musu.

Zanga zanga
Masu zanga zangar Oktoba sun bayyana bukatu 17. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin bukatun kamar yadda tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Tinubu ba zai tsoma baki a rigimar NNPCL da Dangote ba'

Bukatun masu zanga zangar Oktoba 17

1. Sakin masu zanga zanga

Matasan sun bukaci a saki dukkan wadanda aka kama a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa a watan Agusta, a bude musu asusun bakuna da kuma biya su fansar tsare su da aka yi.

2. Sauke wasu jami'an gwamnati

Matasan sun bukaci a sauke ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, Sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun da kwamishinan yan sanda na Abuja.

3. Rusa tsarin mulkin 1999

Haka zalika sun bukaci Bola Tinubu ya rusa tsarin mulkin Nijeriya na 1999 domin kawo sabo da zai saukaka rayuwa.

4. Gyara a majalisun tarayya

Masu zanga zanga sun bukaci a rusa majalisar dattawa da kuma mayar da majalisar wakilai ta rika aikin wucin gadi.

5. Karin albashi

Matasan sun bukaci a biya ma'aikatan Najeriya mafi ƙarancin albashi da bai yi kasa da N250,000 ba.

6. Inganta ilimi

Matasan sun bukaci a inganta harkar ilimi kuma a ba yan Najeriya damar yin karatu ba ta hanyar lamuni karatu ba.

Kara karanta wannan

Zanga zangar Oktoba: 'Yan sanda sun fadi dalilin gayyatar shugaban matasa

7. Sakin Nnamdi Kanu

Haka zalika sun bukaci gwamnatin tarayya ta saki Nnamdi Kanu da kuma dauke sojoji a Kudu maso Gabashin Najeriya.

8. Dawo da kadarorin gwamnati

A cikin bukatun, matasan sun bukaci a dawo da dukkan kadarorin gwamnati da aka sayarwa yan siyasa.

9. Dawo da tallafi

Masu zanga zanga sun bukaci gwamnatin tarayya da dawo da tallafi a cikin abubuwan da ta zare shi domin yaki da yunwa.

10. Yaki da rashawa

Cikin bukatun akwai neman hukunta tsofaffin shugabannin Najeriya da ake zargi da sace dukiyar ƙasa.

11. Canza tsarin Najeriya

Haka zalika sun bukaci a canza tsarin mulkin Najeriya ta yadda za a ba yankuna mallakar juya arzikinsu.

12. Yaki da ta'addanci

Sun bukaci a kawo karshen yan bindiga masu garkuwa da mutane a dukkan sassan Najeriya.

13. Gyaran lantarki

Haka zalika sun bukaci a dauki matakin kawo gyara a harkar lantarki a Najeriya.

14. Gyara a hukumar INEC

Kara karanta wannan

'Matsalolin sun yi yawa,' Za a yi taro domin tunkarar Tinubu da murya 1

Matasan sun bukaci gwamnatin tarayya da sauya fasalin hukumar INEC domin rage rashawa a hukumar.

15. Samar da ayyuka

Matasan sun bukaci farfaɗo da masana'antu domin samar da ayyuka ga matasa.

16. Gyara harkar shari'a

Masu zanga zanga sun bukaci a kawo gyara a harkar shari'a domin rage cin hanci da rashawa a cikinta.

17. Zabe a kasar waje

A karshe, matasan sun bukaci kawo tsarin da zai ba yan Najeriya da ke kasashe ketare damar ka da kuri'a a lokacin zabe.

Legit ta tattauna da matashi a Najeriya

Wani matashi a jihar Gombe, Muhammad Sa'idu ya ce matukar za a yi zanga zangar cikin lumana zai shiga.

Muhammad ya ce ya yanke hukuncin ne saboda matsin rayuwa da al'umma suka shiga a fadin Najeriya.

Tinubu ya ba yan Najeriya hakuri

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kara yin kira na musamman ga yan Najeriya kan halin wahalar rayuwa da ake ciki a kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan fara aikin matatarsa: Dangote ya samu kwangilar N158bn daga gwamnatin Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawari nan gaba kadan yan Najeriya za su murmure a kan halin da suke ciki na wahalar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng