BUA: Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Maiduguri Sun Ƙara Samun Tallafin N2bn
- Abdul Samad Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA Group ya ba waɗanda ambaliya ta rutsa da su a jihar Borno tallafin N2bn
- Babban daraktan kamfanin, Kabiru Rabiu ne ya sanar da haka yayin da tawgaar BUA Group ta kai ziyarar jaje ga gwamnan jihar Borno
- Ya ce shugaban BUA Group zai ƙara turo tirela biyar na buhunan shinkafa 900 da wata tirela biyar ta buhunan fulawa 900 da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Maiduguri - Shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, Alhaji Abdul Samad Rabiu ya bayar da tallafin N2bn ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri da Jere a jihar Borno.
Babban daraktan kamfanin, Kabiru Rabiu shi ne ya sanar da haka yayin da ya jagoranci tawagar kamfanin BUA suka kai ziyarar jaje ga Gwamna Babagana Zulum.
Kabiru Rabiu, wanda ya wakilci shugaban kamfanin BUA Group, ya ce tallafin Naira biliyan biyu ya ƙunshi tsabar kuɗi da kuma kayan abinci, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BUA ya bada tallafin kudi da abinci
“Mai girma gwamna, Alhaji Abdul Samad Rabi’u ya aiko mu da tallafin zunzurutun kudi har Naira biliyan daya da kuma kayan abinci na N1bn.
"Baya ga haka, ya ce zai bada tallafin tireloli biyar na buhunan shinkafa 900, tireloli biyar na buhunan fulawa 900 da kuma tireloli biyar na katan 4500 na taliya.
"Ranka ya dade an yi asarar dukiyoyi da rayuka da dama sakamakon wannan bala’i. Muna addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu kuma Ya ba iyalansu karfin jure wannan rashi."
- Kabiru Rabiu.
Zulum ya yabawa shugaban BUA Group
Da yake mayar da martani, Gwamna Zulum ya yabawa attajirin ɗan kasuwar bisa yadda ya tausaya wa jihar Borno a wannan mawuyacin hali da ta tsinci kanta, rahoton The Cable.
Zulum ya kuma godewa shugaban BUA bisa maƙudan kudin da ya bar domin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa, inda ya yi alƙawarin za su isa ga mutanen da ya dace.
Gwamnan Neja ya kai ziyara Maiduguri
A wani rahoton Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya jagoranci tawagar gwamnatinsa da sarakuna sun kai ziyarar jaje Maiduguri a Borno.
A madadin gwamnatin Neja, Mai girma Umaru Bago ya miƙa N250m ga gwamna domin a tallafawa waɗanda mummunar ambaliyar ta rutsa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng