Ambaliya: NDLEA ta Kama Ruɓabɓun Abinci da Magani a Maiduguri

Ambaliya: NDLEA ta Kama Ruɓabɓun Abinci da Magani a Maiduguri

  • Hukumar NDLEA ta kai samame kasuwannin Maiduguri domin tabbatar da ingancin abinci da magani da ake sayarwa bayan ambaliya
  • NDLEA ta ce an samu wasu masu sayar da magani da suka rika sayar da ruɓaɓɓun magunguna ga al'ummar jihar kafin dukar mataki
  • A yanzu haka hukumar NDLEA ta yi nasarar kwato magunguna da abinci na biliyoyin kudi domin ceto rayukan al'ummar Maiduguri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Hukumomi na cigaba da bincike domin tabbatar da lafiya bayan ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri.

Hukumar NDLEA ta ce ta kai samame kasuwannin Maiduguri domin bincike kan abinci da magani da suke sayarwa.

NDLEA
NDLEA ta kama abinci da magani a Borno. Hoto: NDLEA
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa a yayin samamen, NDLEA ta kama abinci da magunguna masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NDLEA ta kai samame kasuwannin Maiduguri

Hukumar NDLEA ta ce ta kammala bincike a kasuwannin Maiduguri kan abinci da magani da ake sayarwa bayan ambaliyar ruwa.

NDLEA ta yi samamen ne a Monday Market, kasuwar Gamboru, kasuwar magani ta Gwange da sauransu.

Jami'an NDLEA sun kama ruɓaɓɓun abinci, magani

Bayan ambaliyar ruwa, NDLEA ta samu bayanai kan yadda wasu ke busar da magunguna da suka jike suke sayarwa al'umma.

Biyo bayan haka hukumar ta bukaci a rufe kasuwanni sai bayan ta yi bincike domin tabbatar da ingancin kayyakkin da ake sayarwa.

Biyo bayan bincike, NDLEA ta kama abinci da magunguna da suka ruɓe na makudan kudi sama da Naira biliyan biyar.

NDLEA za ta cigaba da ƙoƙari a jihohi

NDLEA ta ce za ta cigaba da kokari wajen tabbatar da ingancin abubuwa a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda mutane sama da 100 su ka rasu a manyan iftila'I 4 a Arewacin Najeriya

Hukumar ta kuma yi kira ga al'umma kan sanar da ita duk wani motsi da suka gani da ya saɓa doka domin daukar mataki.

Yan Maiduguri sun fara kwana a titi

A wani rahoton, kun ji cewa biyo bayan ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri da Jere a jihar Borno, mazauna garin da dama sun koma kafa tanti na kan tituna.

Ambaliyar ruwa bayan batsewar madatsar ruwan Alau a ranar 10 ga watan Satumba, ta haddasa barna da raba iyalai da muhallansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng