"Sama da Mutum Miliyan 88 na Fama da Talauci," Sheikh Pantami Ya Ba Matasa Mafita
- Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa mutum miliyan 88.4 ke fama da matsanancin talauci kuma mafi akasari ƴan Arewa ne
- Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya ce ya kamata matasa su su tashi su nemi ƙwarewar fasaha da sana'o'in zamani
- Ya ce bincike ya nuna fasahar AI za ta samar da ayyukan yi miliyan 95 nan da wasu ƴan shekaru kuma za a rasa wasu ayyukan miliyan 83
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zaman, Farfesa Isa Pantami ya bayyana wasu alkaluma masu ban tsoro game da talauci a Najeriya.
Pantami, wanda yana ɗaya daga cikin manyan malumman Musulunci a Najeriya ya ce mutum miliyan 88.4, kimanin kaso 45% na al'ummar ƙasar nan na rayuwa cikin matsanancin talauci.
Kalaman Sheikh Isa Pantami na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tsaro, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan ya jaddada bukatar ƴan Najeriya musamman matasa su tashi tsaye, su nemi gogewa a fannoni daban-daban na ilimin zamani da fasaha.
Pantami ya bayyana haka ne yayin a yake gabatar da wata lakca da aka shirya a bikin cikar jihar Katsina shekara 37 da kafuwa.
"Talauci ya fi yawa a Arewa" - Farfesa Pantami
Ya ce akasarin wadanda ke fama da matsanancin talauci ƴan Arewa ne, wanda hakan ya nuna buƙatar matasa su tashi su nemi ilimin fasaha da sana'o'in zamani.
Fitaccen malamin ya ƙara da cewa a zamanin yanzu, samun takardar karatu ba za ta wadatar da mutum ba, inda ya roƙi matasan da suka gama karatu su duba wasu damarmakin.
A cewarsa, aikin gwamnati da matasa ke nema ido rufe bai wuce kaso 5% na damarmarkin ayyukan da ke akwai ba.
Pantami ya jero hanyoyin samun nasara
Pantami ya ce bincike ya nuna fasahar AI za ta samar da ayyuka miliyan 95 daga nan zuwa 2025, wanda zai maye gurbin ayyuka miliyan 83.
Domin samun nasara, Pantami ya lissafa wasu manyan fannoni da ake so mutum ya samu kwarewa a kansu da suka hada da; zamantakewa, sarrafa tunani da kuma warware matsaloli.
Gwamna Umaru Radda na Katsina ya godewa Pantami bisa amsa gayyata, inda ya ce gwamnatinsa ta riga ta bullo da wasu tsare-tsare da za su inganta goben jihar.
Katsina ta cika shekara 37 da kafuwa
A wani rahoton kuma gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda ta bayyana shirye-shiryen da ta ke yi na gudanar da bikin murnar cika shekaru 37
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Bala Zango ya ce a ranar bikin, Farfesa Isa Ali Pantami zai gabatar da wa'azi a kan rikon amana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng