Wata Tanka Maƙare da Man Fetur Ta Fashe, Ta Yi Wa Mutane Illa a Abuja
- Wata tanka maƙare da man fetur ta fashe a kan dogon titin Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin, 23 ga watan Satumba
- Rahotanni sun nuna cewa wuta ta kama sosai bayan fashewar tankar, lamarin da ya sa mutane guduwa domin neman tsira da rayuwarsu
- Wani ma'aikaci a ɗaya daga cikin asibitocin Maitama ya bayyana cewa an kawo waɗanda lamarin ya rutsa da su domin ba su kulawa da yi masu magani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wata babbar tanka maƙare da man fetur ta fashe ta kama da wuta a Maitama, ɗaya daga cikin manyan unguwanni a babban birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun nuna wasu mutane da ke cikin motar haya a kusa da tankar sun samu raunuka daban-daban sakamakon fashewar yau Litinin, 23 ga watan Satumba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a titin Shehu Shagari, Maitama a babban birnin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tankar ta fashe ta kama da wuta
Wani ganau, Saminu Sani ya bayyana cewa bayan fashewar tankar, sun ga harshen wutar da ta kama ya yi tsini a sararin samaniya.
Ya ce galibin masu ababen hawa sun bar motocinsu a kan titi, sun gudu domin tsira da rayuwarsu daga wutar da ta tashi mai tsananin zafi.
Saminu ya ƙara da cewa lamarin ya haifar da cunkoso a ttitin wanda ya shafi wurare da dama kamar farmers market, Nicon Hilton Hotel, MTN da Chicken house.
Fashewar tankar ya raunata mutane
Wani jami'in lafiya a asibitin da ya fi kusa da wurin a Maitama ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kawo masu mutanen da suka ji raunuka a fashewar tankar.
Mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ya ji wasu daga cikin waɗanda ibtila'in ya rutsa da su na cewa direban tankar da ta fashe ya gudu.
Gobara ta laƙume dukiya a Legas
A wani rahoton kuma mutane da dama sun tafka asara bayan gobara ta tashi a kasuwar katako ta Itamaga a Ikorodu da ke jihar Lagos.
Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa, Nosa Okunbor ya ce gobarar ta jawo mummunan asara na miliyoyi a jihar.
Asali: Legit.ng