Bayan Karin Kudin Fetur, Yan Najeriya na Cikin Barazanar Tashin Kudin Wutar Lantarki
- Tallafin kudin wutar lantarki da gwamnati ta ke biya ya haura N180bn a watan Satumba daga kusan N100bn a Mayu
- Wannan ya jefa yan kasar nan masu shan lantarki a tsarin band A cikin hadarin karuwar farashin wutar da su ke sha
- Hukumar kula da harkokin lantarki ta kasa (NERC) ta dora alhakin hauhawar farashin lantarki kan tashi da saukar Dala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Akwai alamun cewa masu shan wutar lantarki a tsarin Band A da ke samun wutar sama da awanni 20 za su fuskanci kari.
Wannan na zuwa bayan an samu karin kudin tallafin wutar lantarki da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta biya a watan nan.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya za ta biya N181.63bn a watan Satumba daga N102.30bn da ta biya a watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu karin kudin tallafin wutar lantarki
A baya, hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta janye tallafin fetur daga yankunan band A inda su ke biyan N225 duk sa'a.
A wancan lokaci; watan Afrilu 2024, kudin tallafin da gwamnati ta biya wa sauran bangarorin da ke shan wuta ya tashi a N140.7bn
Yadda Dala ke hargitsa farashin lantarki
Hukumar NERC da ke kula da harkokin lantarki ta kasa ta bayyana hawa da saukar farashin Dala a matsayin abin da ke jawo tashi da saukar farashin lantarki.
A watan Yuli, NERC ta bayyana farashin a Dala daya a matsayin N1,494.1, a watan Agusta kuma ya hau zuwa 1,564.3, sai watan Satumba inda ta kai N1601.5
Kamfanin wuta ya kara kudin lantarki
A wani labarin kun ji cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kaduna Electric ya yi karin kudin wuta ga abokan huldarsa da ke tsarin band A.
A sanarwar da kamfanin ya fitar, an ji hukumar kamfanin rarraba lantarkin Kaduna ya yi karin kudin wuta ga 'yan band A daga N206.80/kwh zuwa N209.5kwh.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng